Ganawar ASUU da FG Ta Kammala, Ba a Cimma Wata Matsaya Ta Kirki Ba

Ganawar ASUU da FG Ta Kammala, Ba a Cimma Wata Matsaya Ta Kirki Ba

  • A jiya ne kungiyar malaman jami'a ta gana da wakilan gwamnatin Buhari don kawo karshen yajin aiki
  • ASUU ta shiga yajin aiki tun watan Fabrairun bana, kuma ta shafe akalla kwanaki 184 ba tare da bude jami'o'i ba
  • Daliban Najeriya na ci gaba da kama wasu hanoyin neman kudi tun bayan da yajin aikin ya zama wani abu daban

FCT, Abuja - A ranar Talatar da ta gabata ne aka gana da kungiyar malaman jami’o’i (ASUU) da gwamnatin Buhari, kamar yadda Channels Tv ta ruwaito.

Wasu majiyoyin da ke da masaniya kan lamarin sun shaida cewa tawagar gwamnatin tarayya ta gana da wakilan kungiyar ASUU a hedikwatar hukumar kula da jami’o’i ta kasa ta NUC.

Yadda ganawar ASUU da gwamnatin Buhari ta kaya
Ganawar ASUU da FG Ta Kammala, Ba a Cimma Wata Matsaya Ta Kirki Ba | Hoto: puncng.com
Asali: UGC

A cewar majiyar daga ASUU:

“Ganawar da tawagar FG ta kasance karkashin jagorancin Farfesa Nimi Briggs kuma an fara da karfe 12:00 na rana, an kammala da karfe 3:00 na rana. Babu wani sabon tayi a teburin, kawai dai sun roke mu mu janye yajin aikin ne.”

Kara karanta wannan

Shawari kyauta: Hanyoyi 15 da za ku bi domin kiyaye kanku daga fadawa matsala a Najeriya

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Wata majiya kuwa cewa ta yi kuma wani babban jami'in ma'aikatar ya kuma tabbatar:

"Malaman sun tafi a fusace, duk da cewa ba mu san hakikanin abin da aka tattauna da su ba kamar yadda kuke gani, ba a gayyace mu ba, amma an yi watsi da shawarar da aka gabatar."

Shima da yake tabbatar da faruwar lamarin, wani mamba na kungiyar ASUU ta kasa da ya nemi a sakaya sunansa ya bayyana cewa gwamnati ba ta dauki tattaunawar da muhimmanci ba.

“Ba da gaske suke ba. Ba zan iya yin cikakken bayani gare ku ba saboda shugabanmu na kasa ne ke da alhakin fadin bayanan. Shawarar da aka gabatar babu hankali a cikinta. Babu wani haske a lamarin.”

Da aka tuntubi kakakin ma’aikatar ilimi, Ben Goong ya shaida wa Punch cewa, ministan ilimi zai yi wa manema labarai bayani a ranar Alhamis mai zuwa.

Kara karanta wannan

Ministan Buhari: APC ta gyara kasar nan, kamar ba a taba ta'addanci ba

Tattaunawa bata yi kyau ba

A bangare guda, shugaban ASUU, Farfesa Emmanuel Osodeke ya bayyana cewa yana cikin wata ganawa kuma zai dawo ya yi bayani. Har yanzu bai ce komai ba.

Daga baya a daren ranar Talata, Osodeke a wata tattaunawa da ya yi da daya daga cikin wakilan jaridar ya ce tattaunawar ''bata yi kyau ba''.

Ya kara da cewa:

“Ba mu sanya hannu kan komai ba; ba su zo da wani abu mai kyau ba. Ba zan ba da cikakkun bayanai ba. Za mu fara magana da membobinmu kafin mu yi magana da manema labarai. Muna wakiltar membobinmu ne.''

ASUU ta shiga yajin aikin ne a ranar Litinin, 14 ga watan Fabrairu, 2022 sakamakon gazawar gwamnati wajen biyan wasu bukatun mambobinta.

Kyakkyawan Labari Ga Daliban Najeriya, ASUU Ta Ce Za Ta Gana da FG Kan Batun Janye Yajin Aiki

A wani labarin, kwanaki dari da tamanin da uku bayan da mambobin kungiyar malaman jami’o’i suka fara yajin aikin, shugabanninsu na shirin sake ganawa da tawagar gwamnatin tarayya.

Kara karanta wannan

A shirye muke: ASUU sun sauko, sun ce za su iya janye yaji a yau bayan ganawa da FG

Shugaban kungiyar na kasa, Emmanuel Osodeke a ranar Litinin, 15 ga watan Agusta, ya bayyana cewa ASUU za ta gana da FG domin shawo kan matsalolin da suka shafi yajin aikin a yau Talata 16 ga watan Agusta.

Da yake magana a gidan talabijin na Channels TV a shirin Politics Today, ya ce kungiyar a shirye ta ke ta janye yajin aikin da zarar gwamnatin Buhari ta biya bukatar ta a ganawar da aka shirya gudanarwa a yau.

Asali: Legit.ng

Online view pixel