Tashin Hankali Yayin Da ’Yan ISWAP Suka Sace Manoma 6 a Jihar Borno

Tashin Hankali Yayin Da ’Yan ISWAP Suka Sace Manoma 6 a Jihar Borno

  • Wasu gungun 'yan ta'addan ISWAP sun yi awon gaba da manoma da ke aiki a gonakinsu a cikin makon nan
  • Majiya ta bayyana cewa, manoman da aka sace 'yan gudun hijira ne, kuma suna aiki a gonar da ke da nisa ne da gari
  • 'Yan ta'addan ISWAP da Boko Haram na yawan kai hare-hare yankunan Arewa maso Gabashin Najeriya

Mafa, jihar Borno - Labari mara dadi da muke samu ya bayyana cewa, wasu 'yan ta'adda da ake zargin 'yan ISWAP ne sun sace akalla manoma shida a jihar Borno.

Rahoton jaridar Daily Trust ya ce, an sace manoman ne a karamar hukumar Mafa da ke jihar Borno a Arewa maso Mabashin Najeriya a ranar Laraba 17 ga watan Agusta.

Kara karanta wannan

'Yan sanda sun ceto mutum 4 daga hannun miyagun 'yan bindiga a wata jiha

Yadda 'yan ISWAP suka sace manoma a jihar Borno
Tashin Hankali Yayin Da ’Yan ISWAP Suka Sace Manoma 6 a Jihar Borno | Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

Wani fitaccen mai sharhi ga harkokin tsaro a tafkin Chadi, Zagozola Makama, ya bayyana yadda lamarin ya faru.

A cewarsa, galibi manoman ‘yan gudun hijira ne da aka taba raba su da gidajensu, kuma an sace su a Bulagarji, inda gonarsu take

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An far wa manoman ne da sanyin safiyar ranar Laraba 17 ga watan Agusta a daidai lokacin da suke aiki, kamar yadda wasu dangi suka tabbatar.

Hakazalika, dangin sun ce 'yan ta'addan sun kira waya, kuma sun nemi a ba su kudin fansa mai yawa.

Wani na kusa da ya nemi a sakaya sunansa ya shaida cewa, tsagerun na neman N15m a matsayin kudin fansa, kamar yadda The Nation ta ruwaito.

Bayan shan ragargaza daga sojoji, Boko Haram da ISWAP sun sanyawa jama'a haraji

A wani labarin, rahotanni sun ce mayakan Boko Haram da ISWAP sun nada sabbin kwamandoji tare da sanya sabon haraji ga manoma da 'yan kasuwa da kuma masunta a yankunan.

Kara karanta wannan

Rashin tsaro: Sanatan APC Ya Fadi Tushen Matsala, Yace Gwamnati Ba ta Shirya ba

Jaridar PRNigeria ta ce mayakan sun yi sabbin nade-naden ne bayan kashe shugabannin kungiyoyin biyu da sojojin Najeriya suka yi.

Jaridar ta ce: “Bayan mutuwar Abubakar Shekau da kuma hadewar mayakan, kwamitin Al-Barnawiy ya sake dawo da Ba-Lawan don jagorantar abin da suka kira Daular Islama ta Afrika.”

Asali: Legit.ng

Online view pixel