Yadda Jami’an ’Yan Sanda Suka Ceto Wasu Mutanen da Aka Yi Garkuwa Dasu a Jihar Kwara

Yadda Jami’an ’Yan Sanda Suka Ceto Wasu Mutanen da Aka Yi Garkuwa Dasu a Jihar Kwara

  • Rundunar 'yan sanda ta ceto wasu mutanen da 'yan bindiga suka sace a jihar Kwara a jiya Talata 16 ga watan Agusta
  • Kwamishinan 'yan sanda ya shawarci masu ababen hawa su rage tafiye-tafiyen dare saboda gujewa barna
  • Ana ci gaba da bincike domin ceto sauran mutanen tare da kame 'yan ta'addan da ke aikata barnar

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Jihar Kwara - Rundunar ‘yan sandan jihar Kwara ta ce ta ceto mutum hudu daga cikin mutane shida da aka sace a babbar hanyar Obbo-Ile da Osi a jihar.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sanda, Okasanmi Ajayi, ne ya bayyana hakan a ranar Talata 16 ga watan Agusta a Ilorin, Premium Times ta ruwaito.

An ceto wasu mutum hudu daga hannun 'yan bindiga
Yadda Jami’an ’Yan Sanda Suka Ceto Wasu Mutanen da Aka Yi Garkuwa Dasu a Jihar Kwara | Hoto: premiumtimesng.com
Asali: UGC

Ya bayyana cewa, jim kadan bayan samun labarin abin da ya faru, jami'an 'yan sanda, 'yan banga da mafarauta sun dura wurin da lamarin ya faru domin gano tushen lamarin.

Kara karanta wannan

An Kuma: 'Yan Bindiga Sun Sake Yin Garkuwa da Matafiya da Dama a Jihar Arewa

Yadda aka ceto mutanen

Ya ce motar wadanda abin ya shafa tana dauke ne da kayan abinci kuma an same ta, hakazalika an ga kwanson harsashi mai girman 7.62mm.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Mista Ajayi ya ce, tsananin matsi da 'yan bindigan suka ji yasa suka yi watsi da mutum daga cikin shida da suka sace, Rahoton This Day.

Ya ce nan ba da jimawa ba za a kama 'yan ta'addan, wadanda ake kyautata zaton suna cikin daji tare da sauran biyun da aka sace.

Ya kuma ce:

“Kwamishanan ‘yan sanda, Mista Tuesday Assayomo, ya tabbatar wa iyalan wadanda abin ya shafa cewa za a kubutar da su daga hannun masu garkuwa da mutane.
"Assayomo ya shawarci masu ababen hawa da su guji tafiye-tafiyen dare, musamman a kan kebabbun hanyoyi."

'Yan Bindigan da Suka Sace Kwamishinan Nasarawa Sun Nemi Kudin Fansa N100m

Kara karanta wannan

Duk wanda aka gani a harbe: Gwamnatin Zamfara ta haramta hawa babura a wasu yankuna

A wani labarin, wadanda suka yi garkuwa da kwamishinan yada labarai na jihar Nasarawa Lawal Yakubu sun bukaci a biya su N100m a matsayin kudin fansa.

Jaridar The Nation ta rawaito cewa an sace Yakubu ne a gidansa da ke karamar hukumar Nasarawa Eggon da yammacin ranar Litinin 15 ga watan Agusta.

Wata majiya mai tushe wacce ta nemi a sakaya sunanta, ta tona cewa masu garkuwa da mutanen sun bayyana bukatarsu ne a ranar Talata.

Asali: Legit.ng

Online view pixel