Bayan shan ragargaza daga sojoji, Boko Haram da ISWAP sun sanyawa jama'a haraji

Bayan shan ragargaza daga sojoji, Boko Haram da ISWAP sun sanyawa jama'a haraji

  • 'Yan ta'addan Boko Haram da ISWAP sun bayyana sabbin nade-nade da suka bayan kashe kwamandojinsu
  • Hakazalika sun fitar sabon jadawalin haraji ga jama'a, inda suka ambaci manona, 'yan kasuwa da masunta
  • A kwanakin nan Boko Haram suka bayyana cewa sun hade domin ci gaba da kai munanan hare-harensu

Rahotanni sun ce mayakan Boko Haram da ISWAP sun nada sabbin kwamandoji tare da sanya sabon haraji ga manoma da 'yan kasuwa da kuma masunta a yankunan.

Jaridar PRNigeria ta ce mayakan sun yi sabbin nade-naden ne bayan kashe shugabannin kungiyoyin biyu da sojojin Najeriya suka yi.

KARANTA WANNAN: Sunday Igboho Ya Tura Sako Ga FG, Yana Neman Diyyar Makudan Kudade

Bayan Nada Sabbin Kwamandoji, Boko Haram da ISWAP Sun Sanyawa Jama'a Haraji
Kwamandojin Boko Haram/ISWAP | Hoto: prnigeria.com
Asali: UGC

Jaridar ta ce:

“Bayan mutuwar Abubakar Shekau da kuma hadewar mayakan, kwamitin Al-Barnawiy ya sake dawo da Ba-Lawan don jagorantar abin da suka kira Daular Islama taAfrika.”

Sannan mayakan za su dinga karbar N5,000 duk wata daga hannun 'yan kasuwa da manoma, masunta kuma za su biya harajin N2,000 ga duk jakar kifi daya.

Mayakan Boko Haram da ISWAP ba su sha da dadi ba a 'yan kwanakin nan, inda sojojin Najeriya ke ci gaba da fatattakarsu a sansanonin da suke buya, sashen Hausa na BBC ta ruwaito.

A ranar Asabar rahotanni sun ce an kashe mayakan kusan 30 a jihar Yobe bayan harin kwatan bauna da suka yi wa ayarin 'yan sanda a kan hanyar Damaturu zuwa Maiduguri.

KARANTA WANNAN: An Cafke Wasu 'Yan Bindiga Bayan Karbar Kudin Fansa Da Kashe Wanda Suka Sace

Sojojin Najeriya sun dakile harin Boko Haram a Dikwa, jihar Borno

A wani labarin daban, Sojojin Najeriya sun yi nasarar dakile wani hari da aka kaiwa Dikwa, wani gari a jihar Borno, da yammacin Talata, PRNigeria ta ruwaito.

Jaridar ta bayar da rahoton cewa, dimbin ‘yan ta’adda dauke da muggan makamai, wadanda ake zargin ‘yan kungiyar aware ta Boko Haram ne, ISWAP, sun mamaye garin a cikin jerin gwanon motocin bindiga.

Sai dai dakarun Sojojin Najeriya da na Rundunar Sojan Sama sun fatattaki 'yan ta'addan tare da dakile shirin na su, kafar watsa labaran ta ruwaito daga wata majiyar tsaro.

Majiyar ta ce an yi musayar wuta tsakanin sojojin Najeriya da ‘yan ta’adda tare da kashe da yawa daga cikin maharan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel