Hanyoyi 15 da za ku bi domin zama lafiya a irin wannan yanayi mai sarkakiya a Najeriya

Hanyoyi 15 da za ku bi domin zama lafiya a irin wannan yanayi mai sarkakiya a Najeriya

Sufeto Janar na ‘yan sandan Najeriya, Usman Baba, ya zuba jami’an tsaro a makarantu, asibitoci, ma’aikatun lafiya, da muhimman wuraren more rayuwa na kasar nan.

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

A cewar BBC Pidgin, IGP, a wata cikin sanarwa da ya fitar, ya bayyana hakan ne yayin da yake nazari kan yanayin tsaro a Najeriya.

Shugaban na ‘yan sanda ya kuma umurci jami’an rundunar da su yi tsarin tsayarwa da bincike da kuma sintiri akai-akai domin rage yawan aikata laifuka a kasar.

Daga nan Baba ya bukaci ‘yan Najeriya da su baiwa jami’an tsaro hadin kai wajen isa ga wurare masu mahimmanci, hanyoyi da kuma al’umma.

Shawarwarin tsaro 15 daga hukumar 'yan sandan Najeriya
Hanyoyi 15 da za ku bi domin zama lafiya a irin wannan yanayi mai sarkakiya a Najeriya | Hoto: businessday.ng
Asali: UGC

Ya yi nuni da cewa irin wannan mataki zai taimaka domin dakile faruwar miyagun laifuka a sassa daban-daban na Najeriya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kara karanta wannan

Goodluck Jonathan ya Fadakar da Mutane a kan Shugabannin da ba za a Zaba a 2023 ba

A kasa ga wasu shawarwarin zaman lafiya guda 15 da 'yan sanda suka bayar

  1. Kada ku lika takardu da alamomi a jikin motarku da ke bayyana inda kuke aiki, musamman idan babbar ma'aikata ko kungiya ce
  2. Kada ku yada hotunan 'ya'yanku sanye da kayan makaranta ko baji a shafukan sada zumunta
  3. Kar ku ke lika kudi a yayin bukukuwa. Ku yi amfani da ambulaf maimakon hakan
  4. Kar ku ke cire kudi ta ATM sakaka N50,000 ta isheku shagalin lokaci guda
  5. Ko da yaushe kuke goge sakwannin banki, kana ku ke yage takardar POS ko ATM da kuka yi amfani dasu. Abu mai sauki ne ku haddace adadin kudin da ke asusun ku
  6. Kada ku yi wasanni ko motsa jiki cik duhu, kuna iya yin hakan tare da wasu idan da bukatar hakan
  7. Koyaushe ku kulle kofofin ku, koda kuwa kuna bukatar kashe janaretanku a bayan gida
  8. Kada ku sanya katin shaidar ku a waje da zagayen ofishin aikinku, babu wanda ke bukatar sanin inda kuke aiki
  9. Ku zama masu gaskiya ga iyayenku ko abokan rayuwar ku, kuma ku sanar da na kusa da ku duk inda za ku ko kuma inda kuke a kowane lokaci
  10. Kada ku tura yaranku waje, su ne abu mai sauki da za a iya yiwa illa
  11. Kada ku zama ne kan gaba a yankinku. Yi kokari ku kasance masu tawali'u tare da ba gudummawar ku daidai gwargwado
  12. Idan kai mai kyauta ne, yi kokarin yin halinka cikin tsanaki, kuma da ladabi kana a sirrance
  13. Kada ku bata lokaci mai yawa a ofis bayan tashi daga aiki. Abu mai sauki ne ku iya karasa ayyukanku a gida
  14. Ko yaushe ku sanya lamarin tsare kai a gaba kuma a duk abin da za a yi
  15. Ku kula da irin rubuce-rubucen da kuke yi a kafofin sada zumunta, musamman abin da ya shafi rayuwar ku

Kara karanta wannan

A karo na biyu: Buhari ya tura sako mai daukar hankali ga ASUU, ya fadi abin da yake so su yi

Yan Bindiga da Masu Kai Musu Bayanai Za Su Fuskanci Hukuncin Kisa, Inji Matawalle Na Zamfara

A wani labarin, gwamnatin jihar Zamfara ta rattaba hannu a kan hukuncin kisa ga duk wanda aka samu da laifin aikata fashi da makami, satar shanu, tsafi, ko kai wa 'yan bindiga bayanan sirri.

Gwamna Bello Matawalle ne ya bayyana hakan a wani sako da ya sanarwa al’ummar jihar a safiyar ranar Talata 16 ga watan Agusta, Punch ta ruwaito.

Matawalle ya ce: “A ranar 28 ga watan Yuni na wannan shekara, na sanya hannu kan kudirin dokar haramtawa da hukunta masu fashi da makami, satar shanu, tsafi, garkuwa da mutane da sauran laifukan da sukashafe su, 2022.

Asali: Legit.ng

Online view pixel