Salman Rushdie da Ya Yi Batanci Ga Annabi Na Can Rai Hannu Rabbana a Asibitin New York

Salman Rushdie da Ya Yi Batanci Ga Annabi Na Can Rai Hannu Rabbana a Asibitin New York

  • Salman Rushdie, wani marubucin da ya yi batanci ga Annabi Muhammadu SAW ya gamu da fushin wani matashi
  • Bayan daba masa wuka, yanzu haka Rushdie na can asibitin New York inda yake kwance jina-jina bai san inda yake ba
  • A baya gwamnatin Iran ta ba da sanarwar ba da lada mai yawa ga wanda ya kashe Rushdie tun bayan wani rubutu da ya yi

New York - Salman Rushdie, marubuci dan Indiya da rubutunsa ya kai ga barazanar kisa daga gwamnatin Iran a shekarun 1980, an caka masa wuka a lokacin da yake shirin gabatar da lacca a kudu maso yammacin jihar New York.

'Yan sanda sun tabbatar da cewa an caka wa Rushdie wuka a sau daya a wuya kana sau daya a cikinsa a ranar Juma'a bayan da wani mahari ya yi zafin naman farmakarsa a kan dandamali.

Kara karanta wannan

Bidiyo: An Kai Hari Ga Salman Rushdie, Shahararren Marubucin Da Ya Yi Batanci Ga Annabi SAW

Halin Salman Rushdie yake a asibiti
Salman Rushdie da Ya Yi Batanci Ga Annabi Na Can Hannu Rabbana a Asibitin New York | Hoto: aljazeera.com
Asali: UGC

Bayan an dauke shi a jirgin sama zuwa asibiti inda ya shafe sa'o'i a dakin tiyata, Rushdie yana kan na'urar numfashi kuma ya kasa magana tun da yammacin Juma'a, Al-Jazeera ta ruwaito.

Andrew Wylie, wakilin littafinsa, ya rubuta a sakon imel da ya aikawa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa:

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

"Mummunan labari ne, da alama Salman zai rasa ido daya; jijiyoyin hannunsa sun yanke; kuma an caka masa wuka ta taba hantarsa kana ta lalace.”

‘Yan sanda sun bayyana wanda ake zargin da wannan hari da suna Hadi Matar mai shekaru 24 daga New Jersey.

Manjo Eugene Staniszewski na 'yan sandan jihar New York ya shaidawa manema labarai a yammacin ranar Juma'a cewa jami'ai ba su da wata alama ta bincika tsuhen manufar Matar, sun dai ce ya yi radin kansa ne na sheke Salman.

Kara karanta wannan

Daga karshe: An kama wadanda ake zargin sun shiga ofishin gwamnan Katsina sun sace miliyoyi

Stacey Schlosser, wacce ta shaida harin, ta shaida wa kamfanin dillancin labaran AP cewa an caka wa Rushdie wuka sau shida zuwa takwas kafin a kama maharin.

An Farmaki Fitaccen Marubuci, Salman Rushdie, Wanda Ya Yi Batanci Ga Annabi SAW

A tun farko, wani mutumi ya kai wa shahararren marubucin nan, Salman Rushdie, hari yayin da yake kan dandamali zai yi jawabi a ƙasar Amurka.

Marubucin, wanda aka shafe tsawon shekaru ana masa bazaranar kisa saboda ya rubuta wani littafi, 'The Satanic Verses,' da ake zargin ya yi batanci ga Annabi SAW, an farmake shi ne a wani gari dake yammacin New York.

A wani bidiyo da Aljazeera ta wallafa, ta ce wani mutumi ya yi fitar burgu zuwa kan dandamalin da Marubucin ke shirin gudanar da Lakca, inda ya rinka bugunsa yana daɓa masa wuka.

Asali: Legit.ng

Online view pixel