Hotuna: Ɗan Sanata Ahmad Sani Yarima ya angwace da budurwarsa ƴar ƙasar Somalia a London

Hotuna: Ɗan Sanata Ahmad Sani Yarima ya angwace da budurwarsa ƴar ƙasar Somalia a London

  • Muhammad Bello, 'dan Sanata Ahmad Sani Yarima, ya angwance da kyakyawar budurwarsa 'yar kasar Somalia
  • An daura musu aure a ranar Juma'a, 5 ga watan Augustan 2022 a babban Masallacin Juma'a dake birnin London
  • Kamar yadda katin daurin auren ya nuna, Fatima Ali ta tabbatar matar Muhammad Bello bayan sallar Juma'a

Labari da duminsa da Legit.ng ke tattaro muku shine na auren 'dan Sanata Ahmad Sani, Yariman Bakura da za a yi a birnin London.

Kamar yadda @fashionseriesng suka fitar a shafinsu na Instagram, an daura auren a ranar Juma'a, 5 ga watan Augustan 2022 a birnin London.

Bakura
Hotuna: Ɗan Sanata Ahmad Sani Yarima zai angwace da budurwarsa ƴar ƙasar Somalia a London. Hoto daga @fashionseriesng
Asali: Instagram

Ya yi wuff da kyakyawar budurwarsa mai suna Fatima Ali 'yar asalin kasar Somalia a babban Masallacin birnin London.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kara karanta wannan

Hotunan kafin aure: Diyar Sule Lamido na jhar Jigawa, zata yi wuff da kwamishina a Zamfara

Hotunan kafin aure: Diyar Sule Lamido na jhar Jigawa, zata yi wuff da kwamishina a Zamfara

A wani labari na daban, Surayya Sule Lamido, diyar tsohon gwamnan jihar Katsina, Sule Lamido, zata amarce da rabin ranta, Yazid Shehu Fulani.

Yazid Shehu Fulani shi ne Turakin Zamfara kuma kwamishinan kasuwanci mai ci a yanzu na gwamnatin jihar Zamfara.

Kyawawan hotunan zukekiyar amaryar tare da kyakyawan angonta sun bayyana inda shafin @fashoinseriesng suka bayyana cewa shirin biki ya kankama kuma yana gabatowa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel