Pantami Ya San Da Karin Farashin Kudin Waya, Za Mu Kara 5% a Harajin Salula - Gwamnatin Buhari

Pantami Ya San Da Karin Farashin Kudin Waya, Za Mu Kara 5% a Harajin Salula - Gwamnatin Buhari

  • Ministan kudi, kasafin kudi da tsarin kasa ta Najeriya Zainab Ahmed ta ce babu gudu babu ja da baya kan batun karin kashi 5 cikin 100 na harajin waya
  • Zainab ta ce majalisar tarayyar Najeriya da majalisar zartarwa na tarayya, FEC, duk sun amince da karin kafin Shugaba Muhammadu Buhari ya rattaba hannu kan sabuwar dokar
  • Ministan ta kuma soki maganar da ministan sadarwa da tattalin arziki, Farfesa Isa Ali Pantami ya yi kan harajin tana mai cewa ya san da maganan harajin da kuma dalilin hakan

Zainab Ahmed, ministan kudi, kasafin kudi da tsarin kasa, ta ce gwamnatin tarayya tana cigaba da shirin aiwatar da karin kashi biyar na haraji kan ayyukan sadarwa, The Cable ta rahoto.

Hakan na zuwa ne bayan suka da aka yi game da aiwatar da harajin.

Zainab Ahmad
Pantami Ya San Da Karin Farashin Kudin Waya, Za Mu Kara 5% a Harajin Salula, In ji Gwamnatin Buhari. Hoto: @thecableng.
Asali: Twitter

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A makon da ta gabata, Isa Pantami, ministan sadarwar da tattalin arzikin zamani ya soki shirin na aiwatar da karin harajin kashi biyar kan harkokin sadarwa a Najeriya.

A cikin wata sanarwa da aka fitar a ranar Alhamis, Yunusa Abdullahi, kakakin ma'aikatar kudi, kasafin kudi da tsarin kasa, ya ambaci Zainab na cewa a wani taron masu ruwa da tsaki da hukumar sadarwa ta Najeriya NCC.

Zainab, wacce ta samu wakilcin Musa Umar, mataimakin direkta, tsarin haraji, na ma'aikatar kudi, kasafin kudi da tsarin kasa na cewa, an sanar da dukkan hukumomin da abin ya shafa game cewa Shugaba Muhammadu Buhari ya amince da aiwatar harajin.

"Game da kalamen Isa Ali Pantami, ministan sadarwa da tattalin arzikin zamani, dangane da karin kashi biyar cikin dari kan harkokin sadarwa, yana da kai a sani cewa an tura takarda na sanar da karin ga ministan sadarwar da sauran ma'aikatun gwamnati da abin ya shafa," a cewar sanarwar.

"Takardar mai lamba F. 17417/VI/286, mai kwanan wata na 1 ga watan Maris na 2022, mai taken "Amincewar matakan karin haraji da garambawul" An tura ta ga ministoci daban-daban har da ministan sadarwa da tattalin arzikin zamani da wasu shugabannin hukumomi.

Tare da Pantami aka yi dokar, Ministan Kudi, Zainab

Ministan ta kuma soki rashin amincewar da ministan (Pantami) ya yi, ta kara da cewa tare da shi aka yi doka Kudin, kamar yadda Vanguard ta rahoto.

"Game da matakin Farfesa Pantami, akwai bukatar tambaya ko ba tare da shi aka dauki matakan da suka haifar da dokar kudin ba, wanda Majalisar Tarayya da Majalisar Zartarwa ta Tarraya, FEC," sanarwar ta kara da cewa.
"Yana da kyau a sani cewa kafin dokar, an tattauna kan dokar Kudin a FEC wanda Farfesa Pantami mamba ne da kuma Majalisar Tarayya. Hakan na nufin Pantami na da hannu wurin kirkirar Dokar na Kudi, wanda ya kunshi karin harajin.

"Don haka, babu wata hujja nuna rashin amincewarsa duba da cewa ko majalisa ba za ta nuna rashin yarda da dokar tunda ita ta fara amincewa da kudirin dokar kudin kafin Shugaba Muhammadu Buhari ya rattaba hannu a kai ta zama doka.
"Duk da cewa Najeriya ce kasa mai tattalin arziki mafi girma a Afirka, sauya wannan arzikin zuwa haraji ya zama kallubale. Wannan dokar da tsarin haraji na kasa da aka yi wa garambawul za su taimaka wurin tabbatar kasar ta samu haraji da zai tallafawa cigaban tattalin arziki."

Ba Zai Yiwu Ba: Pantami Ya Tubure, Ya Ce Ba Zai Bari a Kara Harajin Katin Waya da Data Ba

Tunda farko, Ministan Sadarwa da Tattalin Arziki na Digital Isa Pantami ya yi fatali da sabon yunkurin da gwamnatin tarayya ta yi na kara harajin kashi biyar cikin 100 a harkokin sadarwa.

Idan aka aiwatar da hakan, zai zama 'yan Najeriya za su fara biyan 12.5% cikin 100% a matsayin haraji daga katin waya ko data da suka saya domin amfaninsu, rahoton Punch.

Asali: Legit.ng

Online view pixel