Akwai matsala: Bankin Duniya ya yi Mummunan Hasashe a kan Halin Najeriya

Akwai matsala: Bankin Duniya ya yi Mummunan Hasashe a kan Halin Najeriya

  • Gwamnatin Muhammadu Buhari ta dage a kan biyan tallafi domin hana farashin man fetur tashi
  • Hakan ya jawo gwamnatin Najeriya ba ta samun isassun kudin da ya kamata duk mai ya yi tsada
  • Bankin Duniya ya gargadi gwamnati cewa ya zama dole ta daina biyan tallafi, ta fadada haraji

Abuja - Duk da karancin kudin shiga da Najeriya ta ke fuskanta, gwamnatin Muhammadu Buhari na cigaba da biyan tallafin fetur har yau.

A ranar Laraba, 10 ga watan Agusta 2022, babban bankin Duniya ya fito yana mai gargadin gwamnatin Najeriya game da halin da ta ke shiga ciki.

Punch ta rahoto masanan su na cewa muddin gwamnatin tarayya ba ta fadada wajen karbar haraji ba, kudin da ke shiga asusun kasar ba zai isa ba.

Kara karanta wannan

Gwamnan APC: Ba yadda za a yi Buhari ya ci bashin N1.1tr don biyan bukatun ASUU

Idan a lokacin da farashin gangar mai ya tashi a kasuwar Duniya, gwamnatin tarayya ba ta amfana ba, za a shiga matsala idan farashi ya karye.

Biyan ‘yan kasuwa makudan kudi domin a bar farashin mai da araha yana jawo cikas. Hakan barazana ce ga kafuwar Najeriya a matsayin kasa.

Rajul Awasthi ya bada shawarwari

Wani babban jami’in da ke kula da harkar samun kudin shiga a bankin Duniya, Rajul Awasthi ne ya yi wannan jawabi a wani taro da NESG ta shirya.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Najeriya
Shugaban Najeriya Buhari Hoto: www.bbc.com
Asali: UGC

Mista Awasthi ya gabatar da jawabi a game da haraji da cigaban kasa a ranar Laraba, inda ya nuna cewa ya zama dole a daina biyan tallafin man fetur.

Rahoton yace an yi taron ne ta yanar gizo, kuma manyan masana da masu ruwa da tsaki sun halarta.

Taro ya yi taro, masu ruwa da tsaki sun halarta

Kara karanta wannan

A Karshe, Buhari Ya Yi Magana Kan Abin Da Ya Janyo Yakin Basasa Na 1967, Ya Bayyana Mafita Ga Najeriya

Jami’in PwC, Taiwo Oyedele ya jagoranci zaman da aka yi da wakilai daga kungiyar MAN ta kasa da shugaba a hukumar haraji, Nana-Aisha Obomeghie.

Idan aka kamanta abin da kasa ta ke samu na kudin shiga da karfin tattalin arziki na GDP, Najeriya ce ta karshe a jerin kasashe 115 da aka yi nazari a kansu.

Daga cikin shawarar da Awasthi ya bada shi ne dole a duba harajin VAR da ake karba. Muddin ba ayi haka ba, gwamnati ba ta da wata hanyar illa cin bashi.

Bashi ya fara yin katutu

Sabon rahoton bankin Duniya ya nuna kowace kasa ta na rage adadin bashin da ke wuyanta. Amma Najeriya ta na kara tunkarar matsi ne a yanzu.

Babban bankin Duniyan yana bin Gwamnatin Najeriya bashin fiye da Naira tiriliyan 5 a 2022. Kasar ta zama ta hudu a jerin wadanda ke da tulin bashi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel