Hotuna: An Yi Gobara A Majalisar Tarayyar Najeriya, Kayayyaki Sun Kone
- Wani daki a cikin ginin harabar majalisar tarayyar Najeriya ya kama da wuta a daren ranar Alhamis inda aka yi asarar kujeru, takardu da wasu kayayyaki
- Wani daga cikin ma'aikatan majalisar tare da taimakon jami'an hukumae kwana-kwana sun lashe gobarar kafin ta yadu zuwa wasu dakuna
- Mahukunta a majalisar sun tabbatar da afkuwar lamarin da ba a san musabbabin ba a yanzu amma ana zargin matsala ce ta wutan lantarki ta janyo gobarar
FCT Abuja - Gobara ta lashe wani daki a ginin majalisar tarayyar Najeriya da ke birnin tarayya a Abuja, Leadership ta rahoto.
Gobarar ta faru ne a yammacin ranar Alhamis a bene na biyu, daki na 227, a sabon bangaren majalisar wakilai na tarayya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A cikin sanarwa da ya fitar a daren ranar Alhamis, Agada Emmanuel, direktan watsa labarai na majalisar tarayya, ya ce ana zargin matsalar lantarki ya janyo gobarar, The Punch ta rahoto.
Agada ya kara da cewa nan take an kashe gobarar kuma bata shafi wani daki ba a ginin.
"Gobara ta tashi a yammacin yau a bene ta biyu daki na 227, a sabon sashi na majalisar wakilai na tarayya, sakamakon abin da ake zargi matsalar lantarki ne wanda wani cikin ma'aikatan magatakardar majalisar tarayya ya gano, kuma nan take ya sanar da hukumar kwana-kwana da ke harabar majalisa," sanarwar ta ce.
"Kazalika, an kashe wutar tare da taimakon ma'aikaci da ke bakin aikin wanda nan take ya shiga ofishin ya yi amfani da na'urar kashe gobara ya kashe wutan kafin zuwan jami'an kwana-kwana.
"Hadin gwiwa tare da ma'aikatan kwana-kwanan ya taimaka wutan bai bazu ba kuma aka kashe wutan lantarkin sashin don yin cikakken bincike kan lamarin.
"Ana sa ran bayan bincike da nazari, za a dawo da lantarki a sashin yan majalisar wakilai na tarayyar ba tare da bata lokaci ba."
Ba wannan bane karo na farko da gobara ta fara tashi a ginin na majalisar tarayya.
A shekarar 2018, gobara ta tashi a wani daki a bene na kasa a ginin sanatoci.
Lamarin ya tilastawa sanatocin da ke cikin zauren majalisar su dakatar da zaman ranar.
Ga hotunan a kasa:
Bauchi: Mummunan Gobara Ta Lakume Shaguna 42 a Jami'ar Abubakar Tafawa Balewa
A wani rahoton, a kalla shaguna 42 ne suka kone a Student Centre, ta Jami'ar Abubakar Tafawa Balewa, Bauchi, sakamakon gobara da ta yi sanadin asarar dukiyoyin miliyoyin naira.
Shagunan da suka kone a Block D suna bayan dakin kwanan dalibai mata ne a Yelwa Campus na jami'ar kamar yadda The Punch ta rahoto.
Shagunan da gobarar ta yi wa barna sun hada da shagunan kwamfuta, shagunan aski a shagunan sayar da kayan masarufi.
An rahoto cewa matsalar wutar lantarki ne ya yi sanadin gobarar da ta fara ci daga wani shago guda daya.
Asali: Legit.ng