Gwamnoni Sun Amince Da Korar Ma'aikata 12,000 Domin Tara Naira Miliyan 450

Gwamnoni Sun Amince Da Korar Ma'aikata 12,000 Domin Tara Naira Miliyan 450

  • Ana zargin gwamnatin tarayya zata kori ma’aikatan gwamnatin tarayya kusan 12,000 daga aiki
  • Muddin Gwamnatin Tarayya ta dauki shawarar gwamnoni ma'aikatan gwamnati daga shekaru 50 zuwa sama zasu yi ritay
  • Rahotanni sun bayyana cewa an dauki matakin ne domin tara wa gwamnat tarayya kimanin naira biliyan 450 saboda raguwar kudaden shiga

Abuja - Kimanin ma’aikatan gwamnatin tarayya 11,926 na iya yin bankwana da aikin su nan ba da jimawa ba. Rahoton Buisness Day

Hakan za yiwu ne muddin gwamnatin Najeriya ta aiwatar da daya daga cikin shawarwarin da gwamnonin 36 suka bayar kamar yadda jaridar Premium Times ta wallafa kwanan nan.

Rahoton ya ce gwamnonin sun ba gwamnatin tarayya shawarar cewa ma’aikatan da suka haura shekaru 50 zuwa sama su yi ritaya tare da ba su albashin ritaya na lokaci daya don barin aiki, matakin da ake ganin zai rage wa gwamnati kudaden kashewa.

Kara karanta wannan

Gwamnan APC: Ba yadda za a yi Buhari ya ci bashin N1.1tr don biyan bukatun ASUU

FEDERAL
Gwamnoni Sun Amince Da Korar Ma'aikatan 12,000 Domin Tara Naira Miliyan 450 FOTO Premium Times
Asali: UGC

Gwamnonin sun kuma nuna cewa ya kamata a maye gurbinsu da matasa masu rahusa, hazikan matasa da mata da suka kammala karatun digiri.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Shawarwarin dai na daga cikin shawarwari 33 da gwamnonin suka baiwa gwamnatin Najeriya na hana Najeriya rugujewa

Yayin da gwamnatin tarayya da na jihohi ke lalubo hanyoyin da za a bi wajen tafiyar da yadda ake samun raguwar kudaden shiga ta fuskar karin kudaden da ake kashewa a Najeriya.

Vanguard ta ruwaito cewa wadanda za a kora ma’aikatan gwamnati ne da ke karbar sama da Naira 30,000 kuma masu shekaru tsakanin 50 zuwa sama kamar yadda jaridar VANGUARD ta rawaito.

Shawarar za ta jawo wa gwamnatin tarayya kashe makudan kudade domin kuwa, mafi yawan wadanda za a kora manyan ma’aikatan gwamnati ne.

Shirin ci gaban kasa na shekarar 2021-2025 ya bayyana cewa, kimanin ma'aikatan gwamnati 35,000 ne aka horar da su kan amfani da na'uraR kamfuta, sannan kuma an horas da ma'aikatan gwamnati sama da 9,000 a fannonin inganta aiki.

Kara karanta wannan

Zan Hukunta Duk Kwamandan da Yan Ta'adda Suka Kai Hari Yankinsa, Shugaban NSCDC Ya Ɗau Zafi

Zaben 2023: Sarkin Musulmi Da CAN Sun Rattaba Hannu A Kan Yarjejeniyar Zaman Lafiya

A wani labari kuma Washington - Mai Alfarma Sarkin Musulmin Najeriya Sa’ad Abubakar III da da Kungiyar Kiristocin Najeriya (CAN), sun rattaba hannu akan yarjejeniyar zaman lafiya gabanin babban zabe mai zuwa a 2023. Rahoton VANGUARD

Sun kula yarjejeniyar ne a birnin Washington na kasar Amurka dan kawar da duk fitinar da zata taso da fuskan addinin a lokacin gudanar da zabe.

Asali: Legit.ng

Online view pixel