Zan Hukunta Duk Kwamandan da Yan Ta'adda Suka Kai Hari Yankinsa, Shugaban NSCDC Ya Ɗau Zafi

Zan Hukunta Duk Kwamandan da Yan Ta'adda Suka Kai Hari Yankinsa, Shugaban NSCDC Ya Ɗau Zafi

  • Shugaban hukumar tsaro NSCDC, AA Audi, ya gaya kwamandojin shiyya da jihohi cewa ba ya son sake jin an kai hari kan kadarorin gwamnati
  • Audi, a taron gaggawa da ya kira yau a Abuja, ya ce daga yau duk yankin da aka kai hari laifin kwamandan shiyyar ne da na jihohi
  • A cewarsa, hukumar NSCDC ce a sahun gaba wajen baiwa kayayyakin gwamnati tsaro kuma wajibi su tashi tsaye

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Abuja - Kwamanda Janar na dakarun hukumar tsaro ta Cibil Defence NSCDC, Ahmed Abubakar Audi, ya kira kwamandojin shiyyoyin Najeriya da na jihohi zuwa wani taron gaggawa a Abuja.

Jaridar Punch ta rahoto cewa yayin taron shugaban hukumar tsaron ya nuna damuwarsa kan yadda ake kai hari kan kayayyakin raya ƙasa na gwamnati wanda alhakin su ne kare su.

Tambarin hukumar NSCDC.
Shugaban Hukumar Tsaro NSCDC Ya Shiga Taron Gaggawaa da Manyan Jami'ai a Abuja Hoto: punchng.com
Asali: UGC

Ba zan lamurci kai hari ba daga yau - CG

Jim kaɗan bayan taron, Kwamandan NSCDC na ƙasa, AA Audi, ya umarci kowane kwamanda ya tabbatar duk wasu kadarorin gwamnati da ke yankinsa sun samu ingantaccen tsaro.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Audi ya sanar da su cewa daga yanzu kwamandan shiyya ko na jihohi su za'a ɗora wa laifin duk wani hari da yan ta'adda suka kai kan kayayyakin gwamnati da ke yankin su.

Ya kuma ba da umarnin girke dakaru a duk wasu wuraren da ke kunshe da kayayyakin ƙasa da ayyukan raya ƙasa kamar su layin dogo, filayen jirgin sama, bututu da kuma gidajen gyaran hali.

Leadership ta ruwaito kwamandan na cewa:

"Mun sani cewa NSCDC ce hukumar dake sahun gaba wajen ba kadarorin gwamnati kariya don haka ba zamu ba ƙasar mu kunya ba. Wajibi mu yi komai iya karfin mu wajen kare albarkatun mu."

"Wajibi mu shirya yaƙi da ɓarayin mai da masu fasa bututu da sauran masu aikata manyan laifuka. Mun yanke cewa duk wasu kwamandojin shiyya da jihohi da suka yi bacci wajibi su farka don sauke nauyin ƙasa."
"Saboda haka duk wani kwamanda zai amsa laifin harin da aka kai yankin dake karkashim ikonsa. Daga yau duk wani kwamanda da ya gaza yin abinda ya dace zamu hukunta shi, alhakin kare gidajen gyaran hali na kan ku."

A wani labarin kuma Matakai 33 da Gwamnoni Suka Shawarci Buhari Ya Ɗauka Don Ceto Najeriya Daga Durkushewa

Gwamnonin Najeriya sun shawarci gwamnatin shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari ta ɗauki wasu matakai cikin gaggawa a wani yunkurin rage wahalhalun kasafin kuɗi da ceto ƙasa daga durkushewar tattalin arziki.

Gwamnonin sun gabatar da matakan yayin gana wa da shugaba Buhari a watan da ya shuɗe, rahoton Premium Times ya tabbatar daga wata majiya da bat da ikom faɗin abinda aka tattauna a taron.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel