Gwamnan Dave Umahi: Babu Yadda Za a Yi FG Ta Ci Bashin N1.1trn Don Biyan Bukatun ASUU

Gwamnan Dave Umahi: Babu Yadda Za a Yi FG Ta Ci Bashin N1.1trn Don Biyan Bukatun ASUU

  • Gwamnan Dave Umahi ya caccaki masu kira ga gwamnatin Buhari ta ci bashi a biya bukatun kungiyar ASUU
  • Malaman jami'a sun shafe akalla watanni biyar shuna yajin aiki saboda neman inganta musu wuraren ayyukansu
  • Ana ci gaba da kai ruwa rana game da yajin aikin ASUU a Najeriya, dalibai da iyaye sun shiga damuwa

Abakaliki, jihar Ebonyi - Gwamna David Umahi na jihar Ebonyi, a jiya ya jaddada cewa babu yadda za a yi kasar nan ta ci sabon bashin Naira tiriliyan 1.1, domin biyan bukatar kungiyar malaman jami’o’i (ASUU).

Kungiyar ASUU da ta shafe sama da watanni 5 tana yajin aikin na neman a aiwatar da yarjejeniyar da ta kulla da gwamnatin tarayya a 2009, rahoton Vanguard.

Umahi ya bayyana haka ne a lokacin da ya karbi bakuncin kwamitin amintattu na hukumar ‘yan sandan Najeriya a gidan gwamnati da ke Abakaliki.

Kara karanta wannan

Yajin Aikin ASUU: Ba Dole Ne Sai Kowa Ya Yi Digiri Ba, In Ji Gwamnan APC

Gwamnati ba za ta ci bashi don biyan bukatun ASUU ba, inji gwamnan APC
Gwamnan APC: Babu Yadda Za a Yi FG Ta Ci Bashin N1.1trn Don Biyan Bukatun ASUU | Hoto: vanguardngr.com
Asali: UGC

A cewar Umahi:

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

“Ban ga yadda ba za mu iya zama da shugabannin ASUU ba, mu kawar da wannan matsala dangane da yajin aikin ASUU.”

Ya shawarci gwamnatin tarayya da ta fara da fitar da kaso kadan daga cikin kudaden da ASUU ta bukata a matsayin hanyar samar da mafita mai dorewa kan kalubalen ilimi da kasar nan ke fuskanta.

“Na taba karantawa a shafukan sada zumunta da jaridu, yadda dalibai suka shiga matsala a zaman gida ko kuma su shagaltar da kansu maimakon zama a makarantu.
"Babu yadda za a yi kasar na, Najeriya ta je ta ciyo rancen tiriliyan 1.1 don biyan bukatar ASUU. Akwai rashin hankali sosai a hakan. Shin bukatunsu na gaskiya ne? Eh, amma za mu iya farawa kadan kadan.

Ku fahimta, ku nemo mafita, Umahi ga malaman jami'a

Kara karanta wannan

Ministoci Sun Samu Sabani a Taron FEC, Shugaban Kasa ya Raba Masu Gardama

Hakazalika, ya yi kira ga kungiyar ASUU da gwamnatin Najeriya su zama masu himma wajen ganin an kawo karshen wannan yajin aiki.

Da yake kokawa game da rikon sakainar kashi da jami'an gwamnati ke yiwa kayayyakin da gwamnati ta mallaka, gwamnan ya ce:

“Amma kuma bari in fada baloli a mafi yawan lokuta, mutanenmu ba su da sha’awar kula da ayyukansu na gwamnati.
"Ko nawa kuka tura wadannan jami’o’in, dan har masu amfani da su, masana’antu, masu kula da harkokin gwamnati ba su fara daukar kayayyaki a matsayin nasu ba, abin zai ci gaba da tabarbarewa ko da kuwa nawa gwamnatin tarayya za ta tura musu.”

Ya kuma yi kira ga malaman jami’o’i da su nuna dan fahimtar juna domin a kawo karshen wannan yajin aikin, rahoton Channels Tv.

Yajin Aikin ASUU: Ba Dole Ne Sai Kowa Ya Yi Digiri Ba, In Ji Gwamnan APC

A wani labarin, gwamnan Jihar Ebonyi kuma shugaban kungiyar gwamnonin Kudu maso Gabas, David Umahi ya ce ilimin Jami'a fa ba na kowa da kowa bane, rahoton The Punch.

Kara karanta wannan

Sai Da Na Gargadi Buhari Cewa Zai Lalata Kasar Nan - Khalifa Sanusi

Umahi ya jadada cewa ba adalci bane a yi tsammanin gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari ta ciyo bashin fiye da Naira tiriliyan 1 don biyan bukatun ASUU.

Gwamnan ya yi wannan jawabin ne kan yajin aikin da malaman jami'o'i ke yi, a lokacin da ya karbi bakuncin tawaga daga asusun yan sandan Najeriya karkashin jagorancin Dr Ben Akabueze, a Abakaliki a ranar Laraba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel