Zaben 2023: Sarkin Musulmi Da CAN Sun Rattaba Hannu A Kan Yarjejeniyar Zaman Lafiya

Zaben 2023: Sarkin Musulmi Da CAN Sun Rattaba Hannu A Kan Yarjejeniyar Zaman Lafiya

  • Mai Alfarma Sarkin Musulmin Sa’ad Abubakar da Kungiyar Kiristocin Najeriya CAN sun rattaba hannu akan yarjejeniyar zaman lafiya gabanin zaben 2023
  • Kungiyar Kristocin Najeriya CAN ta ce zata yi aiki tare da Musulmi wajen gujewa tashin hankali lokacin gudanar da zabe
  • Sarikin Musulmi da Kungiyar CAN sun yi alkawarin tsayuwar daka wajen tabbatar an gudanar da zabe na gari

Washington - Mai Alfarma Sarkin Musulmin Najeriya Sa’ad Abubakar III da da Kungiyar Kiristocin Najeriya (CAN), sun rattaba hannu akan yarjejeniyar zaman lafiya gabanin babban zabe mai zuwa a 2023. Rahoton VANGUARD

Sun kulla yarjejeniyar ne a birnin Washington na kasar Amurka dan kawar da duk fitinar da zata taso da fuskan addinin a lokacin gudanar da zabe.

Kara karanta wannan

Kungiyar 'yan Arewa: Kamata ya yi Shettima ya hakura da takara da Tinubu saboda dalilai

Wata gidauniyar samar da zaman lafiya da hadin gwiwar wasu kungiyoyin kare hakkin dan Adam guda 70 suka shirya taron koli na kasa da kasa kan wanzar da ’yancin addini a birnin Washington

A wata sanarwa da Tsohon Shugaban kungiyar Kristocin Najeriya CAN Rabarend Samson Ayokunle ya fitar a ranar Laraba, ya ce bangarorin biyun Musulmi da Kirista za sun yi aiki tukuru dan gujewa tashin hankali kamar yadda Aminiya ta rawaito.

sultan
Zaben 2023: Sarkin Musulmi Da CAN Sun Rattaba Hannu A Kan Yarjejeniyar Zaman Lafiya FOTO THE GUARDIAN
Asali: Facebook

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Samson ya kara da cewa sun amince daura mabiyansu akan tubalin hakuri da juna domin samar da zaman lafiya a kasar baki daya.

Baban Malamin Addinin kirista yace ya san akwai Musulmi da Kiristoci ’yan Najeriya da yawa da ke kyamar tashin hankali, kuma suke bukatar zaman.

Kungiyar CAN da kuma Sarkin Musulmin sun yi alkawarin tsayuwar daka wajen ganin an gudanar da zabe na gari mai cike da adalci.

Kara karanta wannan

Rikici: Kiristocin APC a Arewa sun ta da hankali, dole a kwace tikitin Shettima a ba su

Dole Kujerar Shugaban Kasa ya Dawo Kudu a 2023 - Akeredolu

A wani labari kuma, Jihar Ondo - Gwamnan Jihar Ondo Rotimi Akeredolu yayi ikrarin cewa dole kujerar shugabankasa ya koma yankin Kudu a 2023 saboda kada a saba yarjejeniyar mulkin karba-karba dake tsakanin yankunan kasar. Rahoton PUNCH

Mulkin karba-karba bayan cikin kundin tsarin mulkin Najeriya amma ana amfani da tsarin tun 1999 da mulki ya dawo hannun farar hula saboda haka bai kamata tsarin ya canza ba a yanzu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Tofa avatar

Ibrahim Tofa