Ministoci Sun Samu Sabani a Taron FEC, Shugaban Kasa ya Raba Masu Gardama

Ministoci Sun Samu Sabani a Taron FEC, Shugaban Kasa ya Raba Masu Gardama

  • An tattauna a kan maganar bashin Paris Club da ‘Yan kwangila suke bin Gwamnoni
  • Ministar kudi da AGF sun bukaci a fara janye bashin daga cikin kason Jihohi a asusun FAAC
  • Wasu Ministoci da SGF ba su yarda da hakan ba, a karshe shugaban kasa yace a ajiye maganar

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

FCT, Abuja - Shugaba Muhammadu Buhari ya umarci Ministar tattalin arziki, Zainab Ahmed ta dakatar da cire kudin da ake janyewa na bashin Paris Club.

Wani rahoto na musamman da ya fito daga Premium Times a ranar Talata, 9 ga watan Agusta, yace shugaban kasa ya bada wannan umarni a makon jiya.

Mai girma Muhammadu Buhari ya bada umarnin a taron majalisar zartarwa na FEC wanda aka yi a makon da ya wuce a gaban duk sauran Ministocin tarayya.

Kara karanta wannan

Lauje cikin nadi: Majalisa za ta titsiye ministar kudi kan batun kudaden tallafin man fetur

Kwanakin baya kungiyar gwamnoni na kasa ta NGF ta nemi gwamnatin tarayya ta dakatar da janye bashin da ake bin jihohi daga yarjejeniyar Paris Club.

Gwamonin sun rubutawa sakataren gwamnatin Najeriya, Mr. Boss Mustapha takarda, inda suka nuna masa za a saba doka idan aka cire kudin alhali ana kotu.

Shugaban NGF na kasa, Kayode Fayemi ya zargi Ministan shari’a, Abubakar Malami SAN da Ministar kudi, Zainab Ahmed da laifin saba doka da umarnin kotu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Taron FEC
Taron FEC a Aso Villa Hoto: @Bashir Ahmaad
Asali: Facebook

An nemi a fito da kudin kwangiloli

An nemi a fara janye kudin daga hannun jihohi ne domin biyan ‘yan kwangila kudin ayyukan da suka yi.

Da aka zo zaman FEC a makon jiya, sai aka ji Ministoci sun gabatar da maganar a fara biyan ‘yan kwangilolin kudinsu daga kason gwamnonin jihohi a FAAC.

Raddin Ministoci a FEC

Bayan Ministar kudi ta nemi hakan, sai abokan aikinta irinsu Babatunde Fashola da Festus Keyamo suka yi mata raddi, sannan Boss Mustapha ya tsoma baki.

Kara karanta wannan

Rikicin Atiku da Wike: Jam'iyyar PDP ta dage zaman NEC saboda ta'azzarar rikicin gida

Sauran Ministoci sun fadawa Zainab Ahmed da Malami cewa bai dace a nemi a fara cire wasu kudi da sunan biyan ‘yan kwangila a irin wannan yanayi ba.

Ganin an bijiro da maganar kudin a lokacin da gwamnoni suke neman abin da za su biya ma’aikatansu albashi, shugaban kasa yace ayi watsi da maganar.

Rashin tsaro da 2023

Kun ji labari an samu bayyanar wata kungiya da ta fi karfin ‘yan bindigan da aka sani a wasu jihohin da ke bangaren Arewa da za su iya jawo cikas a zaben 2023.

Abubakar Siddique wanda shi ne Centre for Democratic Development Research and Training (CEDDERT) da ke Zaria ya bayyana wannan dazu a garin Kano.

Asali: Legit.ng

Online view pixel