Mambobin Majalisar Dokokin Katsina Sun Shirya Gana Wa da Masari, Buhari Kan Tsaro

Mambobin Majalisar Dokokin Katsina Sun Shirya Gana Wa da Masari, Buhari Kan Tsaro

  • Mambobin majalisar dokokin jihar Katsina zasu gana da gwamna Masari da shugaba Buhari kan rashin tsaron jihar
  • Majalisar ta cimma wannan matsaya ne yayin da matsalar tsaro ke ƙara taɓarɓarewa a jihar, mahaifar shugaban kasa
  • Wani rahoto ya nun mutane sun fara tashi daga wasu anguwanni a cikin birnin Katsina saboda tsoron kawo hari

Katsina - Majalisar Dokokin Jihar Katsina ta cimma matsayar gana wa da gwamna Aminu Bello Masari, da shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, kan yanayin taɓarɓarewar matsalar tsaro a jihar.

Shugaban kwamitin yaɗa labarai na majalisar, Alhaji Ali Abu Al-Baba, shi ne ya bayyana haka ga manema labarai ranar Talata a Katsina, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Gwamna Masari tare da Buhari.
Mambobin Majalisar Dokokin Katsina Sun Shirya Gana Wa da Masa, Buhati Kan Tsaro Hoto: todayng.com
Asali: UGC

Al - Baba ya bayyana cewa majalisar ta damu matuƙa kan karuwar rahoton ayyukan yan bindigan daji a sassan jihar, wacce take mahaifar shugaban kasa.

Kara karanta wannan

Daga Ƙarshe, Shugaban APC Na Ƙasa Ya Magantu Kan Shirin Majalisa Na Tsige Shugaba Buhari

A cewar ɗan majalisar, kalubalen tsaron da ake fama da shi yanzu haka a jihar babban abun damuwa ne kuma bai kamata a zuba masa ido ba.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Bugu da ƙari ya ce mambobin majalisar zasu tafi kai tsaye su gana da shugaban kasa game da bukatar dake da akwai na lalubo hanyoyi da ɗaukar matakan kawo karshen ayyukan yan bindiga.

A jawabinsa, Honorabul Al- Baba ya ce:

"Wajibi a gaggauta yin wani abu domin dakile ta'addancin yan bindiga. Saboda haka muna rokon samun goyon baya da kuma haɗin kan kowa da kowa a yaƙi da masu tada ƙayar baya."

A halin yanzun, mambobin majalisar dokokin sun nuna goyon bayan su ga kiran gwamna Aminu Masari, wanda ya nemi al'umma su farka daga bacci, su mallaki makaman kare kan su daga yan ta'adda.

Kara karanta wannan

Shugaba Buhari Ya Naɗa Tsohon Ɗan Majalisar Tarayya Daga Kano a Wani Babban Matsayi

Yan bindiga sun kai hari Katsina

A wani labarin kuma 'Yan Bindiga Sun Sake Kai Farmaki Cikin Birnin Katsina da Tsakar Rana, Mutane Sun Shiga Tashin Hankali

Mutane sun tarwatse yayin da suka ga yan bindiga sun shigo Anguwannin su da tsakar rana a birnin Katsina, jihar shugaban ƙasa.

Wasu da abun ya faru a idon su sun bayyana cewa yan bindigan sun biyo ne yayin da suka taso wasu makiyaya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel