Kotu Ta Garkame Wani Basarake Kai Kai Hari Fadar Dan Uwansa Sarki a Kwara

Kotu Ta Garkame Wani Basarake Kai Kai Hari Fadar Dan Uwansa Sarki a Kwara

  • An garkame Basaraken Samora bisa zargin ya haɗa yan daba sun farmaki wani sarkin gargajiya, Oloba na ƙasar Eju a jihar Kwara
  • Yayin zaman Kotun na yau, mai gabatar da ƙara ya faɗa wa Kotun cewa maharan sun illata Oloba da iyalansa sun sace masa kuɗaɗe
  • Kotun da ɗage zaman zuwa watan Satumba kuma ta ba da belin wanda ake ƙara bisa wasu sharuɗɗa

Kwara - Kotu ta ba da umarnin tsare Basaraken Samora, Oba Matthew Idowu Ajiboye bisa zargin kaiwa basaraken gargajiya, Oloba na ƙasar Eju, Alhaji Maroof Afolayan Adebayo, hari har fadarsa dake karamar hukumar Irepodun, jihar Kwara.

A rahoton da hukumar yan sanda ta tattara, Oba Ajiboye tare da wasu mutum biyar, Tijani Musibau, Kuburat Sodiku, Afolayan Sukiru, Usman Raufu, Tunde Arinwoye da Saheed Bello, sun farmaki Oloba da iyalansa da makamai masu haɗari.

Kara karanta wannan

Rashin Tsaro: Yan Majalisar Dokokin Jihar Katsina Zasu Sa Labule da Gwamna da Shugaba Buhari

Taswirar jihar Kwara a Najeriya.
Kotu Ta Garkame Wani Basarake Kai Kai Hari Fadar Dan Uwansa Sarki a Kwara Hoto: dailytrust.com
Asali: Facebook

Daily Trust ta ce rahoton yan sandan ya nuna cewa Oloba da iyalansa sun ji munanan raunuka sandiyyar harin yayin da maharan suka sace abubuwa masu muhimmanci da suka haɗa da kudin gida da kasahen waje.

Mai shigar da ƙara daga hukumar yan sanda, Seun, ya gaya wa Kotun cewa har yanzun suna kan gudanar da bincike kan lamarin don haka kuma suna bukatar a ɗage shari'ar.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Wane mataki Kotun ta ɗauka?

Alkalin Kotun Majistire, Mai shari'a Badmus, wanda ya jagoranci shari'ar ya baiwa wanda ake zargin Beli a kudi N500,000 da kuma mutum biyu da zasu tsaya masa.

A rahoton da jaridar Leadership ta tattara, Alƙalin ya kafa sharaɗin cewa waɗan da zasu tsaya wa Basaraken wajibi su kasance a Anguwar da Kotun take.

Daga nan kuma sai ya sanar da ɗage zaman zuwa ranar 24 ga watan Satumba, 2022, domin a dawo a cigaba da sauraron kowane ɓangare.

Kara karanta wannan

Dirama a Kotu, Wani Mutumi Ya Kai Karar Surukansa, Ya Ce Sun Yi Garkuwa da Matarsa Mai Tsohon Ciki

A wani labarin na daban kuma An Kama Yan Bindiga da Masu Safarar Kwayoyi Sama da 100 a Kaduna Cikin Wata Shida

Sama da mutanen da ake zargi 100 ne suka shiga hannun rundunar yan Bijilanti a jihar Kaduna cikin watanni 6 da suka shuɗe bisa zargin aikata laifuka daban-daban.

Jaridar Channels tv ta rahoto cewa ana zargin mutanen da aikata laifuka da duka haɗa da, ta'addancin yan fashin daji, garkuwa, da safarar miyagun kwayoyi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel