Ondo Amotekun ta Kara Kama Yan Arewa 168 da suka Boye a Karkashin Shanu

Ondo Amotekun ta Kara Kama Yan Arewa 168 da suka Boye a Karkashin Shanu

  • Jami'an Rundunar Amotekun sun kama wasu mutane 168 da ake zargin mahara ne dauke da layu a cikin manyan motoci guda biyu
  • Rundunar Amotekun ta ce, ta sa Matafiyar da ta kama a kwanakin baya su koma daga inda suka fito bayan ta musu bincike
  • Amotekun ta ce sabbin matafiya 168 da ta kama sun fito daga jihohin Kano da Jigawa ba tare wani kwakwaran hujja na shigowa yankin su ba

Jihar Ondo - Rundunar yan Sakai na jihar Ondo, wadda aka fi sani da Amotekun, sun cafke wasu matafiya 168 da ake zargin mahara ne dauke da layu a cikin manyan motoci guda biyu. Rahoton PUNCH

Hakan ya zo ne kwanaki uku bayan da rundunar ta kama wasu mutane 151 da ake zargin maharan ne dauke da laya a boye a cikin buhunan shinkafa a unguwar Sango da ke kan hanyar Akure zuwa Ado.

Kara karanta wannan

Jerin Sunayen Yan Ta'adda 5 Da Suka Kai Kazamin Harin Cocin Owo Inda Suka Kashe Fiye Da Mutum 30

Kwamandan rundunar ‘yan sandan Ondo Amotekun, Akogun Adetunji Adeleye, ya ce an kama matafiyann ne a unguwar Itaogbolu da Iju a karamar hukumar Akure ta Arewa .

A cewar kwamandan matafiyar sun fito ne daga jihohin Kano da Jigawa ba tare da wata kwakwarrar manufar shigowa jihar Ondo ba.

Amotekun
Ondo Amotekun ta kara Kama Matafiya168 da suka Boye a Karkashin Shanu FOTO Tribune Oline
Asali: UGC

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Adeleye ya ce, sai da suka sa wadanda suka kama a baya-bayanan suka koma daga inda suke fito, bayan sun kammala yi musu bincke.

Saboda sun gano yawancin matafiyar ba su da wata hujja na shigowa yankin, amma har yanzu suna ci gaba da kwararowa kamar yadda Channels TV ta rawaito.

Kwamandan Amotekun ya ce a ranar Lahadi, Amotekun ta kama manyan motoci guda biyu inda suka shaida musu cewa suna kan hanyarsu ta zuwa jihar Ondo da shanu. Bayan an musu bincike sosai, sai saka gano cewa a sun boye babura kusan 40 tare da mutane 168 a kwance a karkashin baburan.

Kara karanta wannan

Karin Bayani: An Kashe Yan Sanda 4, An Kona Motocci A Harin Da Yan Bindiga Suka Kai Caji Ofis

Da aka yi musu tambayoyi, babu daya daga cikinsu da ke da adireshin inda za su je kuma babu wanda ya gayyace su.

Ta dalilin haka ne yasa muke zargi sun shigo yankin ne dan neman mafakar da za su tada zaune tsaye.

'Yan Bindiga Sun Kashe Rayuka Uku, Sun Sace Mutane da Dama a jihar Taraba

A wani labari kuma, Wasu yan bindiga sun kai hari garin Bali, hedkwatar ƙaramar hukumar Bali a jihar Taraba, inda suka kashe mutum uku kuma suka sace wasu da dama ranar Lahadi da daddare.

Wasu majiyoyi da yawa a Bali sun shaida wa wakilin Punch cewa yan bindigan sun farmaki jami'ai a shingen bincike da ke kusa da babban Asibitin garin, daga bisani suka hari mutane.

Asali: Legit.ng

Online view pixel