Jerin Mutane 13 da Shagari, Buhari, Sauran Shugabanni Suka Yi Wa Afuwa a Tarihi
- A dokar kasa, Shugaban Najeriya yana da ikon da zai iya yi wa wadanda suka aikata laifi afuwa
- Tun a zamanin Yakubu Gowon da Shehu Shagari aka yafewa Obafemi Awolowo da Emeka Ojukwu
- A zamanin nan an yi wa tsohon Gwamnan jihar Bayelsa Dipreme Alamieyesiegha a shekarar 2011
ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit
A tarihin Najeriya, shugabannin kasar su kan yafewa wasu wadanda aka taba samu da laifi. Bayan wannan afuwa, za su zama tamkar ba su yi laifin ba.
Legit.ng Hausa ta kawo rahoto na musamman na wasu daga cikin shahararrun wadanda gwamnatin tarayya tayi masu afuwa tun daga 1966 har zuwa yau.
1. Obafemi Awolowo
A 1953, Gwamnatin Abubakar Tafawa-Balewa ta samu Obafemi Awolowo da laifin cin amanar kasa, amma Yakubu Gowon ya yafe masa a 1966, ya nada shi Minista.
2. Anthony Enahoro
Bidiyo: An haska bidiyon Hajiya Dada, mahaifiyar Yaradua tana rera addu'o'i ga Yassine da Shehu a wurin liyafa
Cif Anthony Enahoro yana cikin ‘ya ‘yan jam’iyyar AG da aka daure tare da Obafemi Awolowo. Bayan an kifar da gwamnatin Balewa, an yafewa Enahoro a shekarar 1976.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
3. Yakubu Gowon
A lokacin Shehu Shagari ne aka yi wa Janar Yakubu Gowon afuwa. An tuhumi tsohon shugaban kasar da taimakawa Bukar Dimka wajen kifar da gwamnati a 1975.
4. Odimegwu Ojukwu
Gwamnatin Shagari ce dai ta yafewa Odimegwu Ojukwu bayan ya jagorancin Biyafara a yakin basasa. Bayan yi wa sojan afuwa ne ya dawo kasarsa a 1981.
5. Nduka Irabor
6. Tunde Thompson
Ibrahim Badamasi Babangida ya yi wa Nduka Irabor da Tunde Thompson afuwa bayan gwamnatin Muhammadu Buhari ta daure ‘yan jaridan a gidan kurkuku.
7. Olusegun Obasanjo
Da Janar Abdussalami Abubakar ya yi mulki tsakanin 1998 da 1999, ya yi afuwa ga Olusegun Obasanjo da Sani Abacha ya daure, aka fito da shi daga kurkuku.
8. Salisu Buhari
Bayan ya karbi mulki, Olusegun Obasanjo ya yafewa tsohon shugaban majalisar wakilan tarayya, Salisu Buhari laifin badakalar takardar shaida ta sa ya yi murabus.
9. Diepreye S. Alamieyeseigha
A shekarar 2013 gwamnatin Goodluck Jonathan ta tabbatar da afuwa ga tsohon gwamnan Bayelsa, Cif Diepreye S. Alamieyeseigha, wanda majalisa ta tsige daga ofis.
10. Janar Oladipo Diya (rtd.)
11. Abdulkarim Adisa (rtd)
Goodluck Jonathan ya yafewa Oladipo Diya da Abdulkarin Adisa zargin da ake yi masu na yunkurin hambarar da Sani Abacha a lokacin yana rike da mulki.
12. Shettima Bulama
Wani da aka yi afuwa a majalisar koli tare da Alamieyeseigha a watan Maris na 2013 shi ne Shettima Bulama wanda ya rike darekta a tsohon bankin Arewa.
13. Farfesa Ambrose Alli
A 2020 Gwamnatin Muhammadu Buhari tayi shawara da majalisar koli ta kasa, aka amince a yafewa tsohon gwamnan Bende, Farfesa Ambrose Alli laifinsa.
Sauran wadanda aka yafewa laifuffukan da suka yi sun hada da; Anthony Enahoro, Moses Effiong, Manjo E.J. Olanrewaju, Babalola Ajayi da wasu fursunoni 2600.
Legit.ng ta rahoto cewa, baya ga haka, an yi afuwa ga masu mutane 44 da aka taba samu da laifi. A shekarar nan ne aka yafewa mutane fiye da 150 da aka daure.
Dalilin yin afuwar - Buhari
A can kwanakin baya, an ji labari an tattauna da Malam Garba Shehu a game da afuwar da shugaban kasa Muhammadyu Buhari ya yi wa wasu mutum 160.
A cewar kakakin shugaban kasar, sai da majalisar koli tayi tunani kafin a yafewa wadannan mutane. A karshe dai mutane da-dama sun yi tir da matakin.
Asali: Legit.ng