Musulma ta Kammala Digiri a Jami'ar Kiristoci Matsayin Dalibar da Tafi Kowa Hazaka

Musulma ta Kammala Digiri a Jami'ar Kiristoci Matsayin Dalibar da Tafi Kowa Hazaka

  • Wata matashiyar musulma budurwa mai suna Oyeneyi Adiat, wacce ta kammala digiri a matsayin dalibar da ta fi kwazo a jami'ar Bowen ta alakanta nasararta ga Ubangiji
  • Matashiyar budurwa ta yaba tare da jinjinawa jama'ar kirki da suke tattare da ita yayin da suke makaranta kan taimakon da suka yi mata
  • Oyeniyin ta shawarci jama'a da su cigaba da dagewa tare da aiki tukuru inda tace aiki nagari da fawwalawa Allah lamurra ne kan gaba idan ana son samun nasara

Wata matashiyar budurwa 'yar Najeriya mai suna Oyeneyi Adiat, ta zama daliba mafi kwazo da ta kammala karatu a jami'ar Bowen, mallakin Kiristoci.

A wallafar da makarantar tayi a Facebook, dalibar da ta kammala digiri tace ta ga ikon Allah a fannoni daban-daban a lokacin da take dalibar jami'a.

Kara karanta wannan

An Gindaya Sharuda Kafin a Cigaba da Karatu a Kwalejin da aka Kashe Deborah

Bowen University
Musulma ta Kammala Digiri a Jami'ar Kiristoci Matsayin Dalibar da Tafi Kowa Hazaka. Hoto daga Bowen University
Asali: Facebook

Na ga ikon Allah

Ta bayyana cewa, a karatun da tayi a makarantar wanda ta kwashe tsawon shekaru bakwai da watanni tara, ta samu manyan nasarori.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wani abu da Allah yayi mata baiwa da shi a matsayinta na daliba shi ne:

"Na samu baiwar abokantaka da alaka mai kyau da jama'a. Baiwar mutane zan iya cewa."

A yi aiki tukuru

Adiat ta cigaba da shawartar jama'a da cewa, komai mutum zai iya idan ya yarda da Allah, yayi aiki tukuru tare da sakankancewa.

A yayin rubuta wannan rahoton, daruruwan mutane sun yi martani kan wallafar a kafar sada zumuntar zamanin.

Legit.ng ta tattaro muk wasu daga cikin tsokacin jama'a.

Funmilayo Nosiru tace: "Ina taya ki murna kyakyawa, Ubangiji zai cigaba da taimakon ki. Cigaba da haskawa."
Kayode Odumuyiwa yace: "Kiristoci sun da karbar mutane tare da hakuri da su. Ba a san ko sau nawa ta kwafsa ba a muhawararta da Kiristocin makarantar amma a'a, Yarabawa ba haka suke ba. Makarantar Kiristoci ce, ba ko kwarzane, babu nadama amma mun godewa Ubangiji."

Kara karanta wannan

Matar Marigayi Alaafin Na Oyo Ta Dawo Daga Saudiyya Kawai Sai Ta Tarar Da Kyautar Mota Daga Wani Bawan Allah

Ras kwana uwar lissafi: Bankin duniya ya dauka nauyin karatun hazikar Bakanuwar yarinya

A wani labari na daban, an sake daukar nauyin karatun Saratu Dan-Azumi, karamar yarinya daga jihar Kano wacce ta kware a lissafi.

A cikin kwanakin nan ne aka gano cewa yarinyar da ta bar makaranta amma take iya sarrafa lambobi kamar kwamfuyuta.

Gidauniyar Bashir Ahmad, tsohon hadimin shugaban kasa ne ya fara daukar nauyin yarinyar.

Wannan daukar nauyin karatun ya zo ne daga Adolescent Girls Initiative for Learning and Empowerment, shirin da bankin duniya ke taimakawa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel