Ras kwana uwar lissafi: Bankin duniya ya dauka nauyin karatun hazikar Bakanuwar yarinya

Ras kwana uwar lissafi: Bankin duniya ya dauka nauyin karatun hazikar Bakanuwar yarinya

  • Saratu Dan-Azumi, karamar yarinyar da ta bar makaranta kuma take iya lissafi kamar kwamfuyuta, ta sake samu an dauka nauyin karatunta
  • Wannan daukar nauyin karatun da aka yi a cikin kwanakin nan ya zo ne daga Adolescent Girls Initiative for Learning and Empowerment
  • AGILE shiri ne na bankin duniya kuma ya nemo tare da samo yarinyar a Kano tare da daukar nauyin karatunta

Gaya, Kano - An sake daukar nauyin karatun Saratu Dan-Azumi, karamar yarinya daga jihar Kano wacce ta kware a lissafi.

A cikin kwanakin nan ne aka gano cewa yarinyar da ta bar makaranta amma take iya sarrafa lambobi kamar kwamfuyuta.

Gidauniyar Bashir Ahmad, tsohon hadimin shugaban kasa ne ya fara daukar nauyin yarinyar.

Saratu Dan Azumi
Ras kwana uwar lissafi: Bankin duniya ya dauka nauyin karatun hazikar Bakanuwa. Hoto daga @BashirFund
Asali: Twitter

Wannan daukar nauyin karatun ya zo ne daga Adolescent Girls Initiative for Learning and Empowerment, shirin da bankin duniya ke taimakawa.

Kara karanta wannan

Shirin 2023: Atiku ya ba da Dino Malaye babban matsayi a tawagar kamfen dinsa

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Jami'in sadarwa na shirin, Aliyu Yusuf, ya ce shirin zai saka Saratu a makaranta.

A kalaman Yusuf: "A ziyarar da tawagar ta kai masarautar Gaya, an gayyaci yarinyar da iyayenta zuwa fadar sarki.
"Wakilan ma'aikatar ilimi ta jihar da tawagar AGILE sun yi bayani ga Sarkin, Alhaji Ali Ibrahim-Abdulkadir, kan niyyar shirin na dauka dukkan dawainiyar karatun yarinyar."

Na bar makaranta ne saboda azzalumai, Saratu tace

A yayin martani kan labarin me dadi, Saratu ta sanar da cewa ta bar makaranta lokacin tana aji hudu na firamare saboda zaluntarta da 'yan ajinsu ke yi.

Tace ta shirya komawa makaranta amma ba za ta koma tsohuwar makarantarta ba inda 'yan ajinsu ke cin zalinta.

A kalamanta:

"Na iya lissafi, tarawa, debewa, rabawa ko ninkawa. Zan iya lissafa lambobi har zuwa miliyoyi da kai ba tare da amfani da kalkuleta ba.

Kara karanta wannan

Ba za ta sabu ba: Kungiyar kiristoci ta fara yaki da ci da addini, za ta ba da katin shaida ga malamai

"Na bar makaranta ne saboda masu cin zali. Sa'o'ina kan kira ni da sunan da bana so. Ba zan koma waccan makarantar ba. Zan yi farin ciki idan na cigaba da karatuna a wata makaranta."

Gidauniyar Bashir Ahmad Ta Dauki Nauyin Karatun Yarinya Mai Baiwar Lissafi Tun Daga Firamare Har Zuwa Jami’a

A wani labari na daban, Allah ya tarbawa garin wata karamar yarinya yar asalin jihar Kano nono, inda ta samu tallafin karatu kyauta tun daga Firamare har zuwa jami’a.

Saratu Dan-Azumi kamar yadda aka bayyana sunanta, ta kasance hazikar yarinya wacce Allah ya yiwa baiwar hada lissafi duk da karancin shekarunta.

Gidauniyar tsohon mai baiwa shugaban kasa Muhammadu Buhari shawara kan harkokin sadarwar zamani, Bashir Ahmad ne ya dauki nauyin karatun Saratu bayan ya samu yardar mahaifanta.

Asali: Legit.ng

Online view pixel