Kano: Mahaifin Hanifa, Yarinyar Da Shugaban Makarantarsu Ya Kashe Ya Ziyarci Sakatariyar NUJ Don Godiya

Kano: Mahaifin Hanifa, Yarinyar Da Shugaban Makarantarsu Ya Kashe Ya Ziyarci Sakatariyar NUJ Don Godiya

  • Mahaifin, Hanifa, daliba yar shekara biyar da shugaban makarantarsu ya halaka ta a Jihar Kano ya kai ziyara ofishin kungiyar yan jarida, NUJ, a Kano
  • Abdulasalam Abubakar, wanda ya kai ziyarar a ranar Juma'a ya ce ta tafi yin godiya ne saboda rawar da kafafen watsa labarai suka taka wurin ganin an kamo wadanda suka halaka yarsa da yanke musu hukunci
  • Ya ce babu kalaman da zai iya amfani da su don nuna godiyarsa inda ya yi addu'ar Allah ya saka wa yan jaridar saboda yin aikinsu yadda ya dace ya kuma ce shi da iyalansa ba za su manta karamcin da aka musu ba

Kano - Abdulsalam Abubakar, mahaifin daliba yar shekara biyar, Hanifa, wanda shugaban makarantarsu ya kashe, ya kai ziyarda sakatariyar kungiyar yan jarida, NUJ, na Kano a ranar Juma'a don godiya kan rawar da kafar watsa labarai ta taka wurin ganin an yiwa yarsa adalci cikin gaggawa.

Kara karanta wannan

Ganduje zai cika alkawari, zai rattaba hannu domin rataye wanda ya kashe Hanifa

Hanifa Abdulsalam Abubakar.
Kano: Mahaifin Hanifa, Yarinyar Da Shugaban Makarantarsu Ya Kashe Ya Ziyarci Sakatariyar NUJ Don Godiya. Hoto: @daily_trust.
Asali: UGC

Ya ce ba za a iya kwatanta muhimmancin rawar da kafafen watsa labarai suka taka ba wurin ganin an yi adalci ga yarsa da wasu suka kashe.

Abubakar ya ce:

"Kafafen watsa labarai sun tabbatar an yi adalci ba tare da bata lokaci ba, yayin shariar, an samu makasan da laifi, an kuma yanke musu hukunci.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

"Ina tunanin babu kalaman da zan iya amfani da su wurin gode wa yan jaridan Najeriya saboda bibiyar labarin kisar ya ta, daga ranar da aka kashe ta har ranar da aka yanke hukunci.
"Za mu dade ba mu manta abin da kuka yi min da iyali na ba, abin da zan kara kawai, shine Allah ya saka muku da alheri saboda saukan nauyin aikinku. Dalilin ziyara ta shine gode wa yan jarida bisa rawar da suka taka don ganin an kama wadanda suka kashe ya ta kuma sun girbi abin da suka shuka."

Kara karanta wannan

Bidiyon Ango Ya Zurfafa Cikin Tunani Yayin Da Amaryarsa Ke Girgijewa A Wajen Liyafar Aurensu

Ya kara da cewa an kula zumunci tsakaninsa da kafafen watsa labarai, kuma da izinin Allah, za a rike zumuncin.

Kotu Ta Yanke Wa Abdulmalik Tanko Hukuncin Kisa Ta Hanyar Rataya

Tuna farko, kun ji cewa kotu ta yanke wa Abdulmalik Tanko, hukuncin kisa ta hanyar rataya bayan samun shi da laifin kashe Hanifa Abukabakar, yar kimanin shekara biyar.

BBC Hausa ta rahoto cewa Alƙalin Babbar Kotun, Mai shari'a Usman Na'abba, wanda ke jagorantar shari'ar kisan ne ya yanke hukuncin a yau Alhamis, 28 ga watan Yuli, 2022.

An tuhumi Tanko, shugaban makarantar da yarinyar ke karatu da yin garkuwa da ita tun a watan Disamba, 2021, daga bisani kuma ya kashe ta, kuma ya ɓinne ta a ɗaya daga cikin makarantunsa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel