Kotu Ta Yanke Wa Abdulmalik Tanko Hukuncin Kisa Ta Hanyar Rataya

Kotu Ta Yanke Wa Abdulmalik Tanko Hukuncin Kisa Ta Hanyar Rataya

  • Babbar Kotun jihar Kano ta yanke wa Abdulmalik Tanko da Hashimu Isiyaku hukuncin kisa ta hanyar rataya bisa kashe Hanifa
  • Ta kuma yanke wa Fatima hukunci bisa kamata da laifin haɗin kai wajen garkuwa da yarinyar yar shekara biyar
  • An tuhumi shugaban makarantar su Hanifa da garkuwa da ɗalibarsa, daga bisani ya kashe ta da taimakon Hashimu

Kano - Kotu ta yanke wa Abdulmalik Tanko, hukuncin kisa ta hanyar rataya bayan samun shi da laifin kashe Hanifa Abukabakar, yar kimanin shekara biyar.

BBC Hausa ta rahoto cewa Alƙalin Babbar Kotun, Mai shari'a Usman Na'abba, wanda ke jagorantar shari'ar kisan ne ya yanke hukuncin a yau Alhamis, 28 ga watan Yuli, 2022.

Abdulmalik Tanko.
Kotu Ta Yanke Wa Abdulmalik Tanko Hukuncin Kisa Ta Hanyar Rataya Hoto: dailytrust
Asali: UGC

An tuhumi Tanko, shugaban makarantar da yarinyar ke karatu da yin garkuwa da ita tun a watan Disamba, 2021, daga bisani kuma ya kashe ta, kuma ya ɓinne ta a ɗaya daga cikin makarantunsa.

Kara karanta wannan

Takarar Yan Addinin Daya Makirci Ne Na Mayar Da Krista Komabaya - Sabon Shugaban CAN

Kotun ta bayyana cewa ta samu Tanko da laifin kulla yadda za'ayi garkuwa da yarinyar, sace ta da kuma kashe ta.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Haka zaliƙa Kotun ta kama Hashimu Isyaku da laifin ba da haɗin kai wajen kisan Hanifa, ɓoye laifin sace ta da kuma masaniyar garkuwa da yarinyar amma ya yi gum da bakinsa.

Bayan haka, Kotun ta kama Fatima Jibril da laifin tana da masaniyar sace Hanifa kuma da ita aka haɗa baki wajen garkuwa da ita, amma ta wanke ta daga zargin ƙin rubuta wasika don sanar da iyayen yarinyar.

Wane hukunci Kotu ta yanke wa kowannen su?

Waɗan da ake zargin sun nemi Kotu ta musu sassauci bayan sauraron dukkan laifukan da aka same su da alikata wa a shari'ar.

Da farko Kotun ta yanke wa shugaban makaranta, Abdulmalik Tanko, hukuncin kisa ta hanyar rataya kan laifin kisan Hanifa da kuma ɗaurin shekara 5 na garkuwa da ita.

Kara karanta wannan

Allah yasa a zartar: Martanin 'yan Najeriya bayan yankewa makashin Hanifa hukuncin kisa

Ta kuma yanke wa Hashimu Isiyaku hukuncin zama gidan Yari na shekara biyu, daga bisani kuma a kashe shi.

Daga karshe, Kotun ta yanke wa Fatima hukuncin ɗaurin shekara biyu a gidan Yari saboda ita uwa ce.

“Wacce ake zargi ta uku kuma a matsayinta na uwa an yanke mata hukuncin daurin shekara daya kan laifin yunkurin garkuwa da wata shekara daya kan hadin baki,” inji alkalin kotun.

Legit.ng Hausa ta zanta da wani Lauya mai zaman kansa, Barinta Tukur Badamasi, mazaunin Kaduna kuma ya shaida mana cewa har yanzun Tanko na da dama idan hukuncin be masa ba.

A cewar lauyan, duk da babbar Kotu ta yanke masa hukunci ba zai yuwu a zartar masa ba har sai gwamna ya sanya hannu.

Barista Badamasi ya shaida wa wakilin mu cewa:

"A tarihin Najeriya gwamnoni ba su cika sa hannu a zartarwa da wani hukuncin kisa ba, tsohon gwamnan Edo, Adams Oshiomhole, ne ya taba zartarwa. Duk da haka shi wanda aka yanke wa hukunci yana da damar zuwa gaba."

Kara karanta wannan

An yi adalci: Mahaifin Hanifa ya yi martani bayan hukunta malamin da ya kashe masa diya

Sai dai Lauyan ya ƙara da cewa duba da ɗanyen aikin da ya aikata kuma kan ƙaramar yarinya da kuma yadda duniya ta yi ca kan shari'ar, zata iya yuwu wa a zartar masa da hukuncin.

A wani labarin kuma Wani Mummunan Hatsarin Mota Ya Ritsa da Mataimakin Kwamishinan Yan Sanda

Ƙaramin mataimakin kwamishinan yan sanda a jihar Kwara, ACP Abolade Oladigbolu, ya rasu sanadin haɗarin mota.

Kakakin yan sandan jihar ya ce Marigayin ya hau ɗan Acaɓa ne sakamakon motarsa na gareji ta samu matsala.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel