Labari Da Duminsa: Yan Bindiga Sun Sace Sarki A Najeriya Bayan Sun Harbi Direbansa

Labari Da Duminsa: Yan Bindiga Sun Sace Sarki A Najeriya Bayan Sun Harbi Direbansa

  • Wasu yan bindiga da ba a san ko su wanene ba sun kai wa basarake a Jihar Ondo hari sun harbi direbansa a kai sun kuma yi awon gaba da sarkin da wasu mutum uku
  • Majiyoyi sun tabbatar da afkuwar lamarin misalin karfe 6.30 na yammacin ranar Alhamis a yayin da Cif Mukaila Bello da wasu ke hanyarsu na zuwa Akure daga Ikare
  • Kakakin rundunar yan sandan Jihar Ondo, Funmilayo Odunlami, ta tabbatar da sace basaraken ta kuma ce tawagar jami'an tsaro sun bazama a garin da nufin ceto wadanda aka sace da kama wadanda ake zargi

Jihar Ondo - Yan bindiga sun sace mutane hudu ciki har da basarake na Iku Quaters, Oniku na IKu, a Ikare Akoko ta Jihar Ondo, Cif Mukaila Bello, Leadership ta rahoto.

Kara karanta wannan

2023: Ana Kokarin Kawo Karshen Rikicin Jam’iyyar PDP, Atiku Ya Zauna da Wike

Tare da basaraken, an cewar wata majiya, an kuma sace Mr Adeniran Adeyemo, Mr Bashiru Adekile da Cif Gbafinro.

Taswirar Jihar Ondo
Labari Da Duminsa: Yan Bindiga Sun Sace Sarki A Najeriya Da Wasu Mutum 3. Hoto: @MobilePunch.
Asali: UGC

Channels TV ta rahoto cewa an sace su ne daren ranar Alhamis a Ago Panu na Owo-Ikare Road, a hanyarsu ta zuwa Akure daga Ikare.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An rahoto cewa maharan sun harbi direban motan kuma yana can a asibiti ana masa magani a Owo.

Kawo yanzu masu garkuwar ba su tuntubi iyalan wadanda suka sace ba a lokacin hada wannan rahoton, amma wani iyalin daya cikin wadanda abin ya shafa ya tabbatar wa manema labarai afkuwar lamarin a Akure.

Rundunar yan sanda ta tabbatar

Kazalika, rundunar yan sandan jihar ta bakin kakakinta, Funmilayo Odunlami, ta ce rundunar ta samu kiran neman dauki misalin 6.30 na yammacin Alhamis kan lamarin.

Odunlami ta ce lamarin ya faru kusa da Ago Yeye, kan Owo-Ikare Road a jihar, ta kara da cewa jami'an tsaro sun bazama don ceto wadanda aka sace da kama wadanda ake zargi.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Allah ya yiwa fitaccen tsohon shugaban 'yan sandan Najeriya rasuwa

Kalamanta:

"Yan bindiga sun bude wuta ga wata mota kirar Toyota Corolla mai rajista NO. KAK 818 AE, lokacin tana tafiya. Harsashin ya sami direban a kansa hakan yasa motar ta tsaya, sauran wadanda ke cikin motan su 4 (ba a san ko su wanene ba) an sace su cikin daji an bar direban a wurin.
"Yan sanda sun gano motar an kuma kai direban asibiti. A yanzu direban ya fara samun sauki yayin da yan sanda da bijilante da mafarauta ne bincika dazuka don ceto wadanda aka sace da kama maharan."

Yan Bindiga Sun Sace Tsohon Dan Majalisar Najeriya A Gidansa

A wani rahoton, yan bindiga a karamar hukumar Ihiala na Jihar Anambra sun sace tsohon dan majalisar dokokin jiha, Benson Nwawulu, The Punch ta rahoto.

Nwawulu dan majalisar dokokin jiha ne wanda ya yi wa'adi biyu a majalisar dokokin jihar Anambra.

Tun bayan barin kujeransa a shekarar 2019, ya sake yin takara amma bai yi nasara ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel