'Ni Na Rika Yi Wa Yan Bindiga Magani,' Fasinjar Jirgin Kaduna Da Ya Samu Yanci Ya Magantu

'Ni Na Rika Yi Wa Yan Bindiga Magani,' Fasinjar Jirgin Kaduna Da Ya Samu Yanci Ya Magantu

  • Daya daga cikin mutanen da aka kubutar daga hannun yan ta'adda da suka sace su a jirgin kasar Kaduna zuwa Abuja ya fadi halin da suka shiga
  • Mustapha Imam, wanda ma'aikaci ne a Jami'ar Usmanu Danfodiyo da ke Sokoto ya ce ba zai yi wa makiyinsa fatan shiga irin bala'in da suka shiga ba
  • Imam ya ce shine ya zama likita a sansanin ya rika yi wa yan bindiga da sauran fasinjojin da aka kama su tare magani duk da cewa babu kayan aiki a sansanin

Mustapha Imam, daya daga cikin mutanen da yan bindiga suka sace jirgin kasar Kaduna zuwa Abuja ya ce ya yi wa yan bindiga magani a lokacin da ya ke tsare a hannunsu.

Kara karanta wannan

Har yanzu akwai harsashi a ciki na: Bidiyon labarin fasinjan jirgin Abd-Kad a hannun 'yan bindiga

Tunda farko Legit.ng ta rahoto cewa an sake sako biyar cikin fasinjojin a ranar Talata.

Mustapha Imam.
'Ni Na Rika Yi Wa Yan Bindiga Magani,' Fasinjar Jirgin Kaduna Da Ya Samu Yanci Ya Magantu. Hoto: Desert Herald
Asali: Twitter

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A wani bidiyon da Tukur Mamu, mawallafin Desert Herald wanda ya taimaka wurin tattaunawa don ganin an sake su, fasinjan ya bayyana zamansa a hannun yan bindigan a matsayin 'lamari matukar muni'.

Imam, wanda ma'aikaci ne a jami'ar Usman Danfodiyo da ke Sokoto, ya ce ba zai yi wa makiyinsa fatan shiga halin da ya tsinci kansa ba.

"Halin da na shiga ba dadi. Kamar yadda ka gani, yanzu na gama zubar da hawayen farin ciki. Na yi murna cewa na samu yanci kuma zan koma tare da iyali na nan bada dadewa ba," in ji shi.
"Ba zan yi wa makiyi na fatan shiga halin da na shiga a watanni hudu da suka shude ba. Wata uku da rabi na farko muna cikin matukar yunwa. Akwai ranakun da sau daya muke cin abinci.

Kara karanta wannan

An Sha Fama: Bidiyon Yadda Wani Ango Ya Yi Sujjada Tare Da Fashewa Da Kuka A Wajen Daurin Aurensa

"Ni ne likita a sansanin. Ina yi wa fasinjojin da yan ta'addan magani.
"Babu magani a sansanin. Akwai wata mata da ta rika suma saboda babu maganin zazzabin cizon sauro."

Ya yi kira ga gwamnati ta yi duk mai yiwuwa don ceto sauran wadanda ke tsare.

"Ina son in yi kira ga gwamnati ta yi duk mai yiwuwa don ceto sauran mutanen da ke tsare," ya kara da cewa.

Ga bidiyon a kasa:

An Kama Matar Ɗan Bindiga a Katsina Da N2.4m, Mijin Ya Tsere Ya Bar Ta

A wani labarin, yan sanda a jihar Katsina sun kama wata matar aure, Aisha Nura, mai shekaru 27 dauke da kudi Naira miliyan 2.4 na cinikin makamai da aka sayarwa yan bindiga, The Punch ta ruwaito.

An kama Aisha, da aka ce matar dan bindiga ne, a ranar 25 ga watan Yuli a yayin da ta ke shirin hawa kan babur din haya (acaba) daga Batsari zuwa kauyen Nahuta.

Kara karanta wannan

Zulum: Fatara Da Talauci Na Iya Sa Wadanda Ke Sansanin Gudun Hijira Shiga Boko Haram

Mai magana da yawun yan sandan jihar Katsina, SP Gambo Isah, ya tabbatar da hakan a ranar Juma'a.

Asali: Legit.ng

Online view pixel