Buhari, Tinubu, IGP, Oyetola, Da Sauran Su Sun yi Jimamin Mutuwar Tafa Balogun

Buhari, Tinubu, IGP, Oyetola, Da Sauran Su Sun yi Jimamin Mutuwar Tafa Balogun

  • Shugaba Buhari ya mika gaisuwar ta’aziyyar sa ga rundunar yan sandan Najeriya, yan uwa da abokan arzikin tsohon sufeto-Janar na ‘yan sandan Najeriya Tafa Balogun da ya rasu
  • Buhari ya yaba kokarin Balogun na ganin ‘yan sanda sun yi aikin su yadda dace a karkashin tsarin dimokradiyya
  • Tafa Blagun ya rasu ne a ranar Alhamis da misalin karfe 8:30 na daren a wani asibiti da ke Lekki a Jihar Lagos bayan gajeruwar jinya

Abuja - A jiya ne shugaba Buhari ya mika gaisuwar ta’aziyyar sa ga rundunar yan sandan Najeriya, yan uwa da abokan arziki na tsohon sufeto-Janar na ‘yan sandan Najeriya Tafa Balogun da ya rasu a ranar Alhamis. Rahoton The Nation

Shima dan takarar shugabankasa a jam'iyyar APC, Asiwaju Bola Tinubu, Sufeto Janar Usman Baba da gwamnan jihar Osun, Adegboyega Oyetola sun mika na su sakon ta’aziyar.

Kara karanta wannan

ImpeachBuhariNow: Yadda Ma'abota Facebook Ke Goyon bayan tsige Shugaban Najeriya

Tsohon Babban Sufeton ‘Yan-sandan Nijeriya, Mustapha Balogun, wanda aka fi sani da Tafa Balogun ya rasu bayan wata gajeruwar jinya a Lagos, yana da shekara 74.

Balogun
Buhari, Tinubu, IGP, Oyetola, da sauran su sun yi Jimamin mutuwar Tafa Balogun FOTO Legit.NG
Asali: UGC

Tafa Balogun ya rasu ne a ranar Alhamis da misalin karfe 8:30 na daren a wani asibiti da ke Lekki a Jihar Lagos bayan gajeruwar jinya.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Mai ba shi shawara na musamman kan harkokin yada labarai da wayar da kan jama’a, Mista Femi Adesina ya sanar da sakon.

Buhari, ya tuna yadda Balogun, a lokacin da yake rike da mukamin IG, ya yi iyakacin kokarin sa wajen ganin ‘yan sanda sun yi aikin su yadda dace a karkashin tsarin dimokradiyya.

Sannan kuma kwazonsa ya kara kwarin guiwa ga jami’an a cikin Rundunar wadanda suka yi aiki karkashinsa.

Buhari ya ce tunanin sa yana tare da iyalai, gwamnati da jama'ar jihar Osun, da kuma tsoffin abokan aikin Tafa Bolagun bisa rashin shi da suka yi.

Kara karanta wannan

2023: Ko ba Wike Zan iya nasara a zaben 2023, Atiku ya shaidawa Dattawan PDP

Sultan Ya Fadawa Masu Yiwa Kasa Hidima Cewa Dokar Shariar Musulunci Na Musulmi Ne Kadai

A wani labari kuma, Mai Alfarma Sarkin Musulmi Alhaji Muhammad Abubakar, ya tabbatar wa masu yiwa kasa hidima NYSC na shekararr 2022 a jihar Sokoto cewa dokar Shari’ar musulunci na musulmi na kadai bata aiki ga wanda ba musulmi ba a jihar. Rahoton PUNCH

Sarkin ya bayar da wannan tabbacin ne a ranar Alhamis a fadarsa lokacin da tawagar masu yi wa kasa hidima ta NYSC a jihar karkashin jagorancin kodinetan jihar suka kai masa ziyarar ban girma.

Asali: Legit.ng

Online view pixel