Sultan Ya Fadawa Masu Yiwa Kasa Hidima Cewa Dokar Shariar Musulunci Na Musulmi Ne Kadai

Sultan Ya Fadawa Masu Yiwa Kasa Hidima Cewa Dokar Shariar Musulunci Na Musulmi Ne Kadai

  • Mai Alfarma Sarkin Musulmi Alhaji Muhammad Abubakar ya tabbatar wa masu yiwa kasa hidima na jihar Sokoto cewa Shariar Musulunci na Musulmi ne kadai
  • Masu Yiwa Kasa Hidima NYSC na shekarar 2022 sun kai wa sarkin Musulmi Muhammad Abubakar ziyarar ban girma a fadar sa
  • Sultan Abubalar ya fadawa Masu Bautan Kasa cewa babu wanda zai tilasta wani shiga addinin musulunci ba tare da son ransa ba

Jihar Sokoto - Mai Alfarma Sarkin Musulmi Alhaji Muhammad Abubakar, ya tabbatar wa masu yiwa kasa hidima NYSC na shekararr 2022 a jihar Sokoto cewa dokar Shari’ar musulunci na musulmi na kadai bata aiki ga wanda ba musulmi ba a jihar. Rahoton PUNCH

Sarkin ya bayar da wannan tabbacin ne a ranar Alhamis a fadarsa lokacin da tawagar masu yi wa kasa hidima ta NYSC a jihar karkashin jagorancin kodinetan jihar suka kai masa ziyarar ban girma.

Kara karanta wannan

A Dena Kawo Addini Cikin Siyasa, In Ji Lalong, Shugaban Yakin Neman Zaben Tinubu

Ya kuma ba su tabbacin tsaron lafiyarsu duk da kalubalen tsaro da kasar ke fuskanta da kuma damar yin addinin da suka ga dama.

Sultan
Sultan Ya Fadawa Masu Bautar Kasa Cewa Dokar Sharia Musulunci Na Musulmi Ne Kadai FOTO Legit.NG
Asali: Facebook

Ya ce shari’ar Musulunci ba ta rataya a wuyan wadanda ba musulmi ba, yana mai jaddada cewa babu wanda za a tilastawa shiga musulunci ba tare da son ransa ba.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Ya kuma bukace su da su ci gaba da zama masu bin doka da oda tare da zama abin koyi ga masu tasowa.

Sarkin ya bukace su da su mutunta al'adun al'ummar jihar Sokoto da suka karbi bakuncinsu.

A nasa bangaren, kodinetan NYSC na jihar, Alhaji Muhammad Nakamba, ya ce wadannan rukunin ‘yan NYSC sun yi fice ta fuskar da’a da kuma bin ka’idojin a sansanin NYSC.

Muna Bukatar Shirin Da Zai Daura Mu Sama Da Yan Ta’adda – Osinbajo Ya Fadawa Sojoji

Kara karanta wannan

Rashin Tsaro: Za Mu Raba Lawan Da Kujeransa Idan Ya Kawo Mana Cikas Wurin Tsige Buhari, In Ji Sanatan Najeriya

A wani labaari kuma, Mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo ya ce akwai bukatar gwamnatin Najeriya ta dauki matakin da zai sanya tunanin su gaba da ‘yan ta’adda da ke barna a fadin kasar. Rahoton Channels TV

Ya ce kalubalen tsaro da kasar ke fuskanta a halin yanzu da barazanar da ke kunno kai, yana bukatar sojoji da sauran masu ruwa da tsaki su kasance cikin shiri tare da kara kaimi wajen kirkiran makamai a cikin gida.

Asali: Legit.ng

Online view pixel