Karfin hali: Dan sanda Ya Kashe Wasu ‘Yan Bindiga 2 da Suka Kai Hari Gidansa

Karfin hali: Dan sanda Ya Kashe Wasu ‘Yan Bindiga 2 da Suka Kai Hari Gidansa

  • Wani sufeton ‘yan sanda da ba a bayyana sunansa ba ya harbe wasu ‘yan bindiga biyu a unguwar Orogwe da ke karamar hukumar Owerri ta Yamma a jihar Imo
  • Al’ummar Orogwe ita ce wurin da wasu ‘yan bindiga suka kai farmaki kwanan nan suka kashe mutane bakwai
  • Hukumomin ‘yan sanda a Imo sun tabbatar wa mazauna garin cewa ‘yan sandan sun dukufa wajen kamo masu laifin tare da tabbatar da tsaron jihar.

Oweei, jihar Imo - An kashe wasu ‘yan bindiga biyu a ranar Alhamis yayin da suka kai hari a gidan wani sufeton ‘yan sanda a garin Orogwe garin da ke a karamar hukumar Owerri ta Yamma a jihar Imo, a kudu maso gabashin Najeriya.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, Michael Abattam ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Alhamis, amma bai bayyana sunan sufeton ‘yan sandan ba, Premium Times ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Allah ya yiwa fitaccen tsohon shugaban 'yan sandan Najeriya rasuwa

Ya ce ‘yan bindigar sun tsallake shingen gidansa ne kana suka shiga harabar gidan inda suka lalata masa kofa, amma sufeton ‘yan sandan ya yi dauki ba dadi dasu.

Yadda jami'in dan sanda ya hallaka 'yan bindiga biyu
Karfin hali: Dan sanda ya kashe wasu ‘yan bindiga biyu da suka kai hari a gidansa | Hoto: thenationonlineng.net
Asali: UGC

Mista Abattam ya ce maharan sun gudu daga wurin a lokacin da sufeton ya fi karfin su, amma an bi su.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewarsa:

"Ana cikin haka, an kashe daya daga cikinsu a wurin, wasu kuma sun tsere zuwa cikin dajin da ke kewaye da mugun rauni."

Kakakin rundunar ‘yan sandan ya ce, nan take sufeto ya sanar da jami’in ‘yan sanda reshen Ogbaku Division, inda ya tura karin jami’ai a yankin.

Da isar jami'ai yankin, sun bi diddigi cikin daji, inda suka ga bindigogi biyu kiran gida da kuma gawar daya daga cikin 'yan bindiga, inji TheCable.

Ya ce katin shaidar da aka gani na daya daga cikin ‘yan bindigar da aka kashe mai suna Chukwuemezie Chukwu, ma’aikacin lantarki ne, wanda ya fito daga Atta a karamar hukumar Ikeduru ta jihar.

Kara karanta wannan

Rashin Kudi Ya Jawo Gwamnoni Sun Ce A Kori Ma’aikata, a Tsuke Bakin Aljihu Kyam

Lamarin dai ya zo ne kwanaki uku bayan da wasu ‘yan bindiga suka mamaye al’ummar yankin tare da kashe jami’an tsaro bakwai.

Mista Abattam ya ce ‘yan bindigar da suka kai wa sufeton hari su ne ‘yan bindigar da suka kai farmaki tare da kashe jami’an tsaro bakwai a unguwar ranar Litinin.

Ya ce an kwashe gawarwakin ‘yan bindigar tare da ajiye su a cibiyar kula da lafiya ta tarayya dake Owerri.

Ya ce ‘yan sanda suna kokarin bincike don zakulo wadanda ake zargin da suka tsere da raunukan harbin bindiga.

Kakakin ‘yan sandan ya bukaci mazauna jihar da su kai rahoto ga ‘yan sanda duk mutumin da aka gani yana jinyar raunukan harsashi ko kuma ya boye a cikin al’ummarsu.

Tashin hankali ga 'yan Arewa mazauna Kudu, 'yan IPOB sun kashe 'yan Nijar 8, sun gudu da kan wani

A wani labarin, tsoro ya shiga wa 'yan Arewa mazauna Owerri, babban birnin jihar Imo, biyo bayan kashe wasu 'yan Nijar takwas da 'yan kungiyar IPOB suka yi.

Kara karanta wannan

Hausawan Arewacin Najeriya na cikin zaman dar-dar a Imo yayin da IPOB suka kashe 'yan Nijar 8

Harin dai ya faru ne a ranar Litinin din da ta gabata lokacin da maharan suka kai hari a wani gini da ke Orogwe, Owerri, wanda galibin Hausawa bakin haure ne daga Najeriya da Jamhuriyar Nijar ke rayuwa a ciki.

‘Yan Arewa a yankin sun ce an kai harin ne saboda IPOB ta dauki dukkan mutanen da ke zaune a yankin ‘yan ci-rani ne daga Arewa, ba tare da sanin wadanda abin ya shafa ba ma 'yan Najeriya bane.

Asali: Legit.ng

Online view pixel