Biki ya yi biki: Bidiyon yadda amarya tayi jifa da gwargwaro da takalmi tana cashewa a bikinta

Biki ya yi biki: Bidiyon yadda amarya tayi jifa da gwargwaro da takalmi tana cashewa a bikinta

  • Wani bidiyo mai bada dariya na yadda wata amarya a Najeriya ta dinga fashewa a ranar aurenta ya janyo cece-kuce a kafafen sada zumuntar zamani
  • A bidiyon da @traditionalweddingng suka wallafa a shafinsu na Instagram, amaryar ta cire gwagwaronta tare da yin jifa da takalmi a wurin rawa
  • Bidiyon ya janyo cece-kuce a kafafen sada zumuntar zamani inda ake cewa amaryar tayi hakan ne don nuna tsabar murnarta a fili

Bidiyon wata amarya tana girgijewa tare da cashewa bayan an saka wakar Kizz Daniels ta Buga a ranar aurenta ya yadu a kafafen sada zumuntar zamani.

A bidiyon mai ban sha'awa, amaryar dake sanye da kayan alfarma amma na gargajiya ta dinga rawan Buga cike da farin ciki tare da annashuwa.

Amarya
Biki ya yi biki: Bidiyon yadda amarya tayi jifa da gwagwaro da takalmi tana cashewa a bikinta. Hoto daga @traditionalweddingng
Asali: Instagram

A yayin rawan, amaryar dake cike da murna ta cire takalmanta kuma hakan ya matukar birge bakin dake rawa tare da ita.

Kara karanta wannan

An Sha Fama: Bidiyon Yadda Wani Ango Ya Yi Sujjada Tare Da Fashewa Da Kuka A Wajen Daurin Aurensa

Kamar hakan bai isa ba, ta cigaba da rawa inda ta cire gwagwaron dake kanta domin ta cashe yadda ya dace.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Babu shakka bidiyon ya janyo martani daban-daban a kafafen sada zumuntar zamani inda mutane suka dinga tafawa amaryar kan yadda ta dage tana rawa.

Bidiyoyi da hotuna: An girgije a liyafar kammala shagalin auren Fatima Shettima da Sadiq Bunu

A wani labari na daban, a ranar Lahadi da ta gabata ne aka yi liyafar cin abincin dare ta kammala bidiri da shagalin auren diyar mataimakin 'dan takarar shugaban kasan Najeriya na jam'iyyar APC, Kashim Shettima, Fatima Shettima da angonta Sadiq Bunu.

Kamar yadda kayatattun hotuna da bidiyoyi suka bayyana, an ga angon da amaryarsa cike da natsuwa cikin shiga ta kamala da alfarma.

A cikin bidiyoyin da @fashionseriesng suka wallafa a shafinsu na Instagram, an ga amarya da angon cikin shigar kaya farare gwanin sha'awa.

Kara karanta wannan

Hotuna da bidiyo: Dankareriyar daham din da Fatima Shettima ta saka wurin wushe-wushe ya dauka hankali

Asali: Legit.ng

Online view pixel