Tsohon Shugaban Jami'ar LASU, Farfesa Hussein, Ya Rasu Yana Shekara 75

Tsohon Shugaban Jami'ar LASU, Farfesa Hussein, Ya Rasu Yana Shekara 75

  • Tsohon Shugaban Jami'ar jihar Legas LASU, Farfesa Lateef Akanni Hussein, ya rigamu gidan gaskiya
  • Bayanai sun nuna cewa tsohon VC ɗin ya rasu ne bayan fama da rashin lafiya na gajeren lokaci yana da shekara 75 a duniya
  • Marigayin ya koyar a jami'ar tarayya da ke Ibadan, kana ya rike shugaban Musulmai na makarantar

Lagos - Tsohon shugaban jami'ar jihar Legas, (LASU), Farfesa Lateef Akanni Hussein, ya riga mu gidan gaskiya, kamar yadda Jaridar The Nation ta ruwaito.

Hussein, wanda Farfesa ne a fannin Physics, ya kasnace VC na Shida a jerin shugbannin jami'ar da aka yi tsakanin 2005 zuwa shekarar 2011.

Farfesa Lateef Akanni Hussein.
Tsohon Shugaban Jami'ar LASU, Farfesa Hussein, Ya Rasu Yana Shekara 75 Hoto: thenationonlineng.net
Asali: UGC

Marigayin ya rasu yana da shekaru 75 a duniya kuma ya kwanta dama ne bayan fama da gajeruwar rashin lafiya da yammacin ranar Lahadi, 31 ga watan Yuli, 2022.

Kara karanta wannan

Daliban Najeriya sun shiga tasku: ASUU ta tsawaita yajin aikinta zuwa karin wasu makwanni masu yawa

Hukumar makarantar ta sanar da labarin rasuwar tsohom VC ɗin a shafinta na dandalin sa da zumunta wato Tuwita ranar Litinin.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Marigayi Farfesa Hussein, ya yi aiki a matsayin Malamin Jami'a a tsangayar koyar da ilimin Physics na jami'ar Ibadan, jihar Oyo.

Haka nan kuma, Marigayin ya taɓa rike shugaban al'ummar Musulmai na jami'ar Ibadan.

ASUU ta tsawaita yajin aiki

Labarin rasuwar tsohon VC ɗin na zuwa ne a dai-dai lokacin da ƙungiyar Malaman Jami'o'i ta ke yajin aiki kan rashin cika mata alƙawurra.

A taron da majalisar ƙoli ta kungiyar ta gudanar ranar 1 ga watan Augusta, 2022, ASUU ta ƙara tsawaita yajin aikin da tsawon makonni huɗu.

Hakan ya biyo bayan rashin cimma matsaya tsakanin ƙungiyar da kuma gwamnatin tarayya ƙarƙashin shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari.

Kara karanta wannan

Tinubu, Dangote, Gwamnoni Da Sauran Manyan Masu Fada Aji Da Suka Halarci Auren Diyar Shettima

A wani labarin kuma Yan Banga Sun Halaka Malamin Makarantar Haddar Alkur'ani a Kano

Yan Banga sun halaka wani Malamin makarantar haddar Alƙur'ani da ake kira Tsangaya a Dabai, ƙaramar hukumar Gwale jihar Kano.

Bayanai sun nuna cewa jami'an tsaron sun hau mutumin da duka ba tare da bincike ba bayan ya tsinci wani jariri.

Asali: Legit.ng

Online view pixel