Tinubu, Dangote, Gwamnoni Da Sauran Manyan Masu Fada Aji Da Suka Halarci Auren Diyar Shettima

Tinubu, Dangote, Gwamnoni Da Sauran Manyan Masu Fada Aji Da Suka Halarci Auren Diyar Shettima

  • Garin Maiduguri da ke jihar Borno ya cika ya tumbatsa a ranar Asabar, 30 ga watan Yuli
  • Gwamnoni, manyan yan kasuwa, manyan gwamnati, sanatoci da sauran masu fada aji sun nunawa Kashim Shettima karamci a auren diyarsa
  • An dai kulla aure tsakanin Fatima Kashim Shettima da Sadiq Ibrahim Bunu wanda ya kasance dan tsohon ministan Abuja

Borno Garin Maiduguri, babban birnin jihar Borno ya cika ya tumbatsa a ranar Asabar yayin da manyan masu fada aji na nesa da kusa suka isa birnin don halartan daurin aure.

An daura auren diyar dan takarar mataimakin shugaban kasa na jam’iyyar APC kuma tsohon gwamnan jihar Borno, Kashim Shettima da dan tsohon ministan Abuja, Ibrahim Bunu.

Shugaban ma’aikatan shugaban kasa, Farfesa Ibrahim Gambari ya halarci daurin auren a madadin shugaban kasa Muhammadu Buhari, jaridar Punch ta rahoto.

Kara karanta wannan

Bidiyon Kashim Shettima Yayin da Yake Sanyawa Diyarsa Fatima Albarka , Ya Yi Mata Kyautar Kudi Da Makulin Mota

Daurin auren Diyar Kashim Shettima
Tinubu, Dangote, Gwamnoni Da Sauran Manyan Masu Fada Aji Da Suka Halarci Auren Diyar Shettima Hoto: The Punch
Asali: UGC

An daura auren ne a fadar Shehun Borno, Mai martaba Alhaji Abubakar Ibn Garbai Umar El Kanemi.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Tsohon gwamnan jihar Bauchi kuma tsohon shugaban PDP na kasa, Alhaji Adamu Mu’azu, shine ya tsaya a matsayin uban ango, yayin da Gwamna Babagana Zulum na jihar Borno ya tsaya a matsayin uban amarya.

Babban limamin masallacin idi na Borno, Shiekh Shettima Mamman Sale be ya daura auren a kan sadaki sisin gwal guda 12.

Manyan mutanen da suka halarci taron sun hada da dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, Bola Tinubu, shugaban majalisar dattawa, Ahmed Lawan, babban mai ba kasa shawara kan harkar tsaro, Janar Babagana Munguno mai ritaya.

Sauran sun hada da manyan masu kudi, Alhaji Aliko Dangote, Alhaji Mohammed Indimi da Alhaji Dahiru Mangal, jaridar The Sun ta rahoto.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu : Tinubu Ya Tafka Kuskure Da Ya Dauki Abokin Takara Musulmi – Yakubu Dogara

Sai Sufeto Janar na yan sanda, Baba Usman Alkali, shugaban APC na kasa, Sanata Abdullahi Adamu; tsohon shugaban APC na kasa, Adams Oshiomhole, shugaban gwamnonin Najeriya, Kayode Fayemi wanda ya wakilci gwamnoni, shugaban kungiyar gwamnonin APC ma ya hallara.

Gwamna Mai Mala Bunin a Yobe, gwamnan jihar Sokoto, Aminu Tambuwal, mataimakin shugaban APC na kasa, Sanata Abubakar Kyari da gwamnan jihar Jigawa, Abubakar Badaru duk sun hallara.

Kimanin sarakunan gargajiya 19 ne suka halarci daurin auren da yan majalisu da manyan jami’an gwamnati.

Bidiyon Yadda Gwamna Zulum Ya Zage Da Kansa Ya Daidaita Cunkoson Jama’a A Wajen Daurin Auren Yar Shettima

A wani labarin, mutanen Kabilar Kanuri na al’adu masu ban sha’awa da ya bambanta su da sauran kabilu da ke yankin arewacin kasar yayin da suke aurar da daya daga cikinsu.

Hakan ce ta kasance a bikin diyar tsohon gwamnan jihar Borno kuma dan takararmataimakin shugaban kasar Najeriya, Kashim Shettima.

Kara karanta wannan

Shagalin Biki Na Manya: Hotuna Da Bidiyo Sun Bayyana Daga ‘Kunshin’ Fatima Shettima

An gudanar da wani shagali na al’ada inda uban amarya ya bayyana a tsakiyar taron mata domin sanyawa diyar tasa albarka a wannan sabuwar rayuwa da ta shiga.

Asali: Legit.ng

Online view pixel