Allah Ya Yi Wa Tsohon Shugaban Rikon Kwarya Na BUK Rasuwa

Allah Ya Yi Wa Tsohon Shugaban Rikon Kwarya Na BUK Rasuwa

  • Farfesa Danjuma Maiwada, tsohon shugaban rikon kwarya na Jami'ar Bayero da ke Kano ya riga mu gidan gaskiya
  • Marigayin ya rasu ne yana da shekaru 70 a duniya bayan gajeruwar rashin lafiya, kuma ya bar matan aure daya da yaya guda tara
  • Shugaban BUK na yanzu, ya hallarci jana'izar kuma ya bayyana halayen kirki na Farfesa Maiwada wanda suka hada da saukin kai, jajircewa wurin aiki ds

Jihar Kano - Tsohon shugaban rikon kwarya na Jami'ar Bayero ta Kano, BUK, Farfesa Danjuma Maiwada, ya rasu yana da shekaru 70 a duniya, Daily Trust ta ruwaito.

Maiwada, wanda ya yi aiki na kankanin lokaci a matsayin shugaban riko na BUK a 2004, dan asalin Jihar Katsina ne amma mafi rayuwarsa a Kano ne inda ya ke koyarwa a jami'ar tun 1976 a tsangayar ilimi.

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: Tsaro ya tabarbare a Imo, Buhari ya ce a tura karin jami'ai da makamai

Innalillahi Wa Inna Illaihi Raji'un: Allah Ya Yi Wa Tsohon Shugaban BUK Rasuwa
Allah Ya Yi Wa Tsohon Shugaban BUK Rasuwa
Asali: Original

A shekarar 2015, ya yi aiki a matsayin shugaban riko na jami'an Northwest University, Kano da yanzu ake kira Jami'ar Yusuf Maitama Sule.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Yana daga cikin masu fada a ji a tsangayar koyar da manya da ilimin addinin musulunci kuma ya koyar da malamai ciki har da shugaban jami'an na yanzu, Farfesa Sagir Adamu Abbas.

Marigayin ya yi ritaya daga aiki a jami'ar a watan Fabrairun wannan shekarar ya kuma gabatar da makala ta ban kwana, inda mutane da dama suka hallara.

Ya rasu ne a ranar Talata bayan fama da gajeruwar rashin lafiya, ya bar matan aure da yaya tara.

Tuni an masa jana'iza bisa koyarwar addinin musulunci.

Abin da shugaban BUK na yanzu ya ce dangaen da marigayin?

Shugaban jami'ar na yanzu, wanda ya hallarci jana'izar ya bayyana Maiwada a matsayin mutum mai saukin kai, karamci da daukan aikinsa da muhimmanci.

Kara karanta wannan

Jarumai 5 da ke jan zarensu a masana'antun Kannywood da Nollywood cike da kwarewa

Ya kuma bayyana shi a matsayin mafi kyawu daga cikin malamai wanda a koyaushe a shirye yake ya taimakawa na kasa da shi.

Matar Shahararren Tsohon Gwamnan Najeriya Ta Rasu a Asibiti a Amurka

A wani labarin, Njideka Ezeife, matar tsohon gwamnan jihar Anambra wanda kuma dattijo ne a kasa, Chief Chukwuemeka Ezeife ta riga mu gidan gaskiya.

Njieka ta rasu ne bayan fama da gajeruwar rashin lafiya a wani asibiti da ke Amurka kamar yadda kungiyar dattawan Igbo ta sanar ta bakin sakatarenta Farfasa Charles Nwekeaku, The Sun ta ruwaito.

Nwekeaku ya ce ana sa ran tsohuwar matar gwamnan za ta dawo Najeriya ne a ranar Litinin, 13 ga watan Disamban 2021 amma kwatsam ta fara rashin lafiya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel