Bidiyoyi da hotuna: An girgije a liyafar kammala shagalin auren Fatima Shettima da Sadiq Bunu

Bidiyoyi da hotuna: An girgije a liyafar kammala shagalin auren Fatima Shettima da Sadiq Bunu

  • An gabatar da kayatacciyar liyafar cin abincin dare ta kammala bidirin auren Fatima Kashim Shettima da Sadiq Bunu
  • A kyawawan hotuna da bidiyoyin da suka bayyana, ango da amaryar sun yi shigar fararen kaya inda suka bayyana cike da kamala
  • Kawaye, abokai da 'yan uwa sun halarci liyafar domin taya su murnar shiga sabuwar rayuwar da zasu yi a wannan makon

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

A ranar Lahadi da ta gabata ne aka yi liyafar cin abincin dare ta kammala bidiri da shagalin auren diyar mataimakin 'dan takarar shugaban kasan Najeriya na jam'iyyar APC, Kashim Shettima, Fatima Shettima da angonta Sadiq Bunu.

Kamar yadda kayatattun hotuna da bidiyoyi suka bayyana, an ga angon da amaryarsa cike da natsuwa cikin shiga ta kamala da alfarma.

Fatima Shettima
Bidiyoyi da hotuna: An girgije a liyafar kammala shagalin auren Fatima Shettima da Sadiq Bunu. Hoto daga @fashionseriesng
Asali: Instagram

A cikin bidiyoyin da @fashionseriesng suka wallafa a shafinsu na Instagram, an ga amarya da angon cikin shigar kaya farare gwanin sha'awa.

Kara karanta wannan

Kyawawan hotuna da bidiyoyin 'ya'ya da jikokin marigayi shugaba Umaru Musa 'Yaradua a wurin bikin 'dan uwansu

Ba su kadai ba, abokai, kawaye da 'yan uwa sun taya ma'auratan murna yayin da suke kokarin shiga sabuwar rayuwa ta aure da ibada.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Hotuna da bidiyo: Dankareriyar daham din da Fatima Shettima ta saka wurin wushe-wushe ya dauka hankali

A wani labari na daban, a yau ranar Asabar, 30 ga watan Yulin 2022 ne za a daura auren Fatima Kashim Shettima da masoyinta Sadiq Bunu.

Tuni shagulgula suka yi nisa inda aka yi liyafar cin abincin dare a Abuja a makon da ya gabata, aka yi saka lalle sannan a jiya Juma'a aka yi wushe-wushe, liyafa ce da 'yan uwa da abokan arziki amma ta al'adar Kanuri.

Babban abunda ya dauka hankalin wadanda suka ga bidiyoyi da hotunan amarya Fatima shine dankareriyar sarkar gwal dake wuyan amarya.

Kara karanta wannan

Bidiyon Kashim Shettima Yayin da Yake Sanyawa Diyarsa Fatima Albarka , Ya Yi Mata Kyautar Kudi Da Makulin Mota

A bidiyoyin da hotunan, sarkar ta yi zaman dirshan a wuyanta inda ta sauko har zuwa kirjinta yayin da ta saka awarwaro suma masu matukar birgewa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel