Kyawawan hotuna da bidiyoyin 'ya'ya da jikokin marigayi shugaba Umaru Musa 'Yaradua a wurin bikin 'dan uwansu

Kyawawan hotuna da bidiyoyin 'ya'ya da jikokin marigayi shugaba Umaru Musa 'Yaradua a wurin bikin 'dan uwansu

  • Tsula-tsulan 'ya'ya da jikokin marigayi shugaba Umaru Musa Yaradua sun haskaka wurin shagalin auren Shehu Yaradua da Yacine Sheriff
  • A hotunan da aka tattaro, an ga matan tsofaffin gwamnoni, Zainab Dakingari da Nafisa Shehu Shema suna walkiya tamkar taurari a wurin taron bikin
  • Hajiya Turai Yaradua ma bata yadda makaman gayunta ba, ta bayyana cike da ado inda take nuna farin cikin ranar tare da jikokin marigayin shugaban kasan

Kyawawan hotuna da bidiyoyin 'ya'ya da jikokin tsohon shugaban kasa, marigayi Alhaji Umaru Musa Yar'adu a wurin shagalin auren Shehu Yaradua sun bayyana.

A hotuna da bidiyoyin da aka tattaro da @weddingstreet_ng a Instagram, 'yan uwan angon sun fito shar da su a wurin shagalin auren 'dan uwansu inda suka dinga haskawa tare da walkiya.

Iyalan Yaradua
Kyawawan hotuna da bidiyoyin 'ya'ya da jikokin marigayi shugaba Umaru Musa 'Yaradua a wurin bikin 'dan uwansu. Hoto daga @theweddingstreet_ng
Asali: Instagram

Iyalan marigayin tsohon shugaban kasan sun hada da matan tsofaffin gwamnonin Najeriya irinsu Nafisa Shehu Shema, Zainab DakinGari da sauransu.

Sun caba ado iyakar kure adaka inda suka saka kaya na alfarma masu matukar birgewa da jan hankali, inda masu kwalliyar zamani suka caba musu kwalliyar kece raini.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Hajiya Turai Yaradua ma ba a bar ta a baya ba, ta caba adonta inda ta fito shar. Ta bayyana a wasu hotuna da ta dauka da 'ya'yanta tare da jikokinta duk a yayin shagalin taya Shehu Yaradua angwancewa.

Bidiyoyi da hotunan raƙashewar 'ya'yan manyan kasar nan a liyafar Yacine da Yaradua, Aisha Buhari ta halarta

A wani labari na daban, a ranar Lahadi, 31 ga watan Yuli 2022 ne aka yi kasaitacciya kuma gagarumar liyafar cin abincin dare ta kammala shagalin auren Shehu Yaradua da amaryarsa Yacine Sheriff.

Duk da an daura auren tun ranar 23 ga watan Yulin 2022, bayan nan an sake balle sabon shagalin bikin wanda ya dinga samun halartar manyan baki a kasar nan.

Gagarumar liyafar ta samu halartar manyan mutane a kasar nan har da uwargidan shugaban kasa Muhammadu Buhari, Aisha Buhari.

Asali: Legit.ng

Online view pixel