Zulum: Fatara Da Talauci Na Iya Sa Wadanda Ke Sansanin Gudun Hijira Shiga Boko Haram

Zulum: Fatara Da Talauci Na Iya Sa Wadanda Ke Sansanin Gudun Hijira Shiga Boko Haram

  • Gwamnan Jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum ya ce fatara da talauci na iya tilastawa wasu da ke sansanin yan gudun hijira shiga kungiyoyin ta'addanci
  • Zulum ya yi wannan jawabin ne wurin taron rufe wasu sansanonin yan gudun hijira a jihar Borno
  • Gwamnan na Borno, ya yi alkawarin cewa kafin wa'adin gwamnatinsa ta kare za a rufe dukkan sansanonin

Borno - Gwamna Jihar Borno, Babagana Zulum ya bayyana fargaba kan karancin kudi da fatara, idan ba a magance shi ba, na iya tilasta wasu mutanen da ke sansanin gudun hijira shiga Boko Haram ko ISWAP, rahoton Daily Trust.

Zulum
Zulum: Fatara Da Talauci Na Iya Sa Wadanda Ke Sansanin Gudun Hijira Shiga Boko Haram. @daily_trust.
Asali: Twitter

Gwamnan, wanda ya bayyana hakan a jiya yayin rufe sansanin yan gudun hijira na Dalori-1, Dalori-2 Gubio da Muna a Maiduguri, ya ce gwamnati ba za ta iya cigaba da ajiye mutanenta a sansanin yan gudun hijirar ba.

Kara karanta wannan

Addu'a Muke Bukata Daga Amurka Ba Wai Su Tsorata Mu Ba, Ministan Buhari

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Ya ce jihar, a karkashin jagorancinsa za ta yi duk mai yiwuwa domin ganin an mayar da mutane gidajensu cikin mutunci.

Zulum ya ce:

"Hanya guda da za a magance matsalar yan ta'adda shine gwamnati ta magance sillar abin wanda ya hada da karuwar talauci, rashin ababen cigaba da matsalar dumamar yanayi.
"Don haka, abin da ya kamata mu yi shine mayar da yan gudun hijira gidajensu cikin mutunci, Ba a tilasta wa kowa komawa gidansa ba, muna farin cikin tallafa musu komawa gidajensu bisa tsarin taron Kampala. Za a tallafawa mutane da sana'a don su cigaba da rayuwarsu idan ba haka ba mutanen mu za su cigaba da zama a sansanin yan gudun hijira," in ji shi.

Gwamnan ya ce za a rufe dukkan sansanin yan gudun hijira kafin wa'adin gwamnatinsa ta kare yana mai kira ga gwamnatin tarayya ta taimaka ta hanyar rage dogaro kan tallafin da ake bawa yan gudun hijirar na matsakaicin zango da dogon zango.

Kara karanta wannan

Ministan farko na sufurin jiragen sama a Najeriya, babban mai kare Nnamdi Kanu ya rasu

Asali: Legit.ng

Online view pixel