Babban magana: An gano 'yan ta'adda na tara makamai za su kai garinsu Buhari

Babban magana: An gano 'yan ta'adda na tara makamai za su kai garinsu Buhari

  • Wasu rahotannin sirri sun bayyana cewa, ana shirin kai hari garin su shugaban kasa Muhammadu Buhari
  • An ce 'yan ta'addan Boko Haram sun hada kayan yaki za su farmaki wasu jihohi a kasar nan cikin kwanaki masu zuwa
  • Ana shan fama da yawaitar kashe-kashe da tashe-tashen hankula a Najeriya musamman a Arewacin kasar

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Najeriya - Jami’an tsaron NSCDC na Najeriya sun ankarar da jama'a kan harin da aka shirya kai wa garinsu shugaban kasa Muhammadu Buhari Katsina, da kuma Legas, babban birnin tarayya, da dai sauransu.

Hukumar NSCDC ta bayyana cewa, 'yan ta'addar Boko Haram da ISWAP, daga bayanan sirrin da ta tattara, sun tattara mayakansu tare da samar da muggan makamai domin aiwatar da wannan mgun aiki.

'Yan ta'adda na shirin kai kazamin hari Katsina
Babban magana: An gano 'yan ta'adda na tara makamai za su kai garinsu Buhari | Hoto: punchng.com
Asali: UGC

Daga makaman da suka tanada akwai na'urorin bugo jiragen sama, manyan bindigogin yaki, da dai sauransu, suna kuma kara shirye-shiryen tunkarar jihar da shugaban kasar ya fito.

Kara karanta wannan

Runduna ta yi martani kan harin 'yan bindiga suka kai kan jami'an fadar shugaban kasa

Wadannan bayanai suna kunshe ne a cikin wani rahoto da aka fito na sirri da aka tira ga duk wasu rundunoni a ranar 25 ga watan Yuli, Punch ta ce ta gani.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Rahoton mai taken, “Martani: Tsananin makirce-makircen da ‘yan ta’adda ke yi na kai hare-hare a sassan kasar nan” ya samu sa hannun mataimakin kwamandan da ke kula da ayyuka na hukumar, DD Mungadi.

Sakon ya ce:

“Mun samu sahihin bayanan sirri cewa Boko-Haram da kungiyoyin ta’addancin ISWAP sun hada mayaka da manyan muggan makamai musamman masu harbo gurneti, da bindigogin yaki da harbo jiragen sama, da manyan bindigogin GPM da su ka yi niyyar turawa domin kai farmaki a jihar Katsina.”

Za a kai munanan hare-hare wasu jihohin Najeriya

Rahoton ya kuma yi ishara da wasu hare-haren da kungiyoyin ‘yan bindiga suka shirya a jihohin Legas, Babban Birnin Tarayya, Kaduna, da Zamfara.

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: DSS Sai Da Ta Gabatar Da rahotannin tsaro 44 Kafin Harin Kuje, In Ji Wase

Ya kara da cewa babban kwamandan rundunar ya umurci kwamandojin jihar da su dauki matakin dakile hare-haren.

A cewar wani yankin rahoton:

“A wani labarin kuma, kungiyoyin ‘yan bindigan guda biyu na shirin kai hare-haren hadin gwiwa a yankin Arewa maso Yamma, Arewa ta Tsakiya da kuma Kudu maso Yamma (Katsina, Zamfara, Kaduna, Kogi, FCT da Legas).

Da aka tuntubi kakakin hukumar NSDC, Shola Odumosu domin jin ta bakinsa, ya yi alkawarin ba da bayani daga baya ga jaridar Punch amma har ya zuwa lokacin hada wannan rahoto bai ce komai ba.

'Yan bindiga sun farmaki jami'an tsaron fadar shugaban kasa bayan barazanar sace Buhari

A wani labarin, kasa da sa'o'i 24 da 'yan ta'adda suka yi barazanar yin garkuwa da shugaban kasa Muhammadu Buhari da gwamnan Kaduna Nasir El'Rufai a wani faifan bidiyo, wasu 'yan bindiga dauke da makamai suka yi wa sojojin na Guards Brigade kwanton bauna a Abuja.

Kara karanta wannan

An samu hargitsi yayin da aka kama wasu 'yan sa kai na bogi a wurin zanga-zangar 'yan kwadago da ASUU

Sojoji uku ne suka jikkata yayin harin wanda ya jefa mazauna birnin tarayya Abuja cikin firgici, rahoton The Nation.

‘Yan bindigar sun nufi makarantar koyon harkokin shari’a ta Najeriya da ke Bwari a lokacin da suka ci karo da jami'an sojojin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel