Karfin hali: 'Yan bindiga sun farmaki jami'an tsaron fadar shugaban kasa bayan barazanar sace Buhari

Karfin hali: 'Yan bindiga sun farmaki jami'an tsaron fadar shugaban kasa bayan barazanar sace Buhari

  • Wasu 'yan ta'adda sun yi yunkurin farmakar jami'an tsaron fadar shugaban kasa a babban birnin tarayya Abuja
  • 'Yan bindiga sun yi barazanar sace shugaban kasa Muhammadu Buhari da gwamnan jihar Kaduna Mallam Nasiru El-Rufai
  • An raunata sojoji uku, kan majiyoyi sun ce jami'an sun yi nasarar dakile harin na 'yan bindiga nan take

Bwari, Abuja - Kasa da sa'o'i 24 da 'yan ta'adda suka yi barazanar yin garkuwa da shugaban kasa Muhammadu Buhari da gwamnan Kaduna Nasir El'Rufai a wani faifan bidiyo, wasu 'yan bindiga dauke da makamai suka yi wa sojojin na Guards Brigade kwanton bauna a Abuja.

Sojoji uku ne suka jikkata yayin harin wanda ya jefa mazauna birnin tarayya Abuja cikin firgici, rahoton The Nation.

‘Yan bindigar sun nufi makarantar koyon harkokin shari’a ta Najeriya da ke Bwari a lokacin da suka ci karo da jami'an sojojin.

Tsageru sun yi yunkurin farmakar jami'an tsaron fadar Buhari
Karfin hali: 'Yan bindiga farmaki jami'an tsaron fadar shugaban kasa bayan barazanar sace Buhari | Hoto: thewillnigeria.com
Asali: UGC

Akwai rahotannin sirri daga majiyar sojoji cewa, ‘yan ta’addan sun dura babban birnin tarayya Abuja da nufin kai hari a makarantar koyon harkokin shari'a da ke Bwari da wasu cibiyoyin gwamnati.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Majiyoyin soji da suka nemi a sakaya sunansu sun ce harin na nuni da cewa ‘yan ta’addan sun mamaye birnin amma hukumomi sun ce saka ido kan motsin maharan.

Wata majiya ta shaidawa Premium Times cewa, biyu daga cikin sojojin da aka kashe manyan jami'ai ne da suka hada da kyaftin da laftanar, yayin da sauran kuwa kananan jami'an sojoji ne.

Hakazalika, rahoton jaridar ya ce mutum bakwai ne aka kashe yayin da jami'ai uku suka jikkata aka kwantar dasu a asibiti.

Yadda aka farmaki jami'an sojojin

A cewar daya daga cikin majiyoyin, wasu da ake zargin ‘yan ta’adda ne sun yi wa dakarun 7 Guards Battalion da ke sintiri a kan hanyar Kubwa zuwa Bwari kwanton bauna.

Ya kara da cewa sojoji uku ne suka jikkata yayin harin kuma an kwashe su zuwa asibitin THE domin kula da lafiyarsu, inji People Gazette.

Majiyar ta ci gaba da cewa:

“Harin kwanton bauna da ya faru a yankin na Bwari ya nuna cewa a zahiri ‘yan ta’addan suna cikin yankin kuma mai yiwuwa ne su aiwatar da shirinsu na kai farmaki a makarantar koyon harkar shari'a da ke Bwari kamar yadda aka ruwaito a baya."

Da aka tuntubi mataimakin daraktan hulda da jama’a na rundunar soji, Kyaftin Godfrey Abakpa, ya tabbatar da cewa wasu da ake zargin ‘yan ta’adda ne sun kai wa sojoji hari amma an samu nasarar dakile su.

Ya kara da cewa an kwashe sojojin da suka samu raunuka zuwa asibiti kuma suna samun kulawa a yanzu.

'Yan sanda: Sai mun kama 'yan ta'adda, amma alkawai sai kuma su sake su

A wani labarin, a wata hira da aka yi dashi, kwamishinan 'yan sandan jihar Kano ya bayyana irin takaicin da yake ji game da alakar 'yan ta'adda da alkalai a Najeriya.

BBC ta zanta CP Sama’ila Dikko, wanda ya bayyana kokawarsa ga yadda ake sakin 'yan ta'adda ba gaira ba dalili bayan kama su da laifi dumu-dumu.

A cewarsa, an sha mika rahoto da karar manyan laifuka ga kotuna mabambanta, amma sai dai jami'an 'yan sanda su ji labarin an ba da belin tsagera ba tare da wani kwakkwaran dalili ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel