'Yan sanda: Sai mun kama 'yan ta'adda, amma alkawai sai kuma su sake su

'Yan sanda: Sai mun kama 'yan ta'adda, amma alkawai sai kuma su sake su

  • Kwamishinan 'yan sanda jihar Kano ya koka ga yadda alkalan Najeriya ke ba da belin 'yan ta'addan da basu da niyyar tuba
  • Kwamishinan ya musanta zargin cewa 'yan sanda ne ke ba 'yan ta'adda da masu aikata manyan laifuka mafaka
  • An sha ganin 'yan ta'addan da suka shiga hannu suna yawo a gari bayan gurfanar dasu a kotu da laifi dumu-dumu

Jihar Kano - A wata hira da aka yi dashi, kwamishinan 'yan sandan jihar Kano ya bayyana irin takaicin da yake ji game da alakar 'yan ta'adda da alkalai a Najeriya.

BBC ta zanta CP Sama’ila Dikko, wanda ya bayyana kokawarsa ga yadda ake sakin 'yan ta'adda ba gaira ba dalili bayan kama su da laifi dumu-dumu.

A cewarsa, an sha mika rahoto da karar manyan laifuka ga kotuna mabambanta, amma sai dai jami'an 'yan sanda su ji labarin an ba da belin tsagera ba tare da wani kwakkwaran dalili ba.

Kara karanta wannan

Bidiyo: Ɗan dambe ya lakaɗi matashin da ya zungure shi a Twitter kuma ya bi shi har gida su goge raini

'Yan sanda sun koka kan yadda ake sakin 'yan ta'adda
'Yan sanda: Sai mun kama 'yan ta'adda, amma alkawai sai kuma su sake su | Hoto: bbc.com
Asali: UGC

Da wakilin BBC ke zantawa dashi game da matsalolin da ya samu a aikinsa, Dikko ya ce:

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

"Matsalar da na samu shine yadda muke kama masu laifi, manya-manyan laifuka, ba kadan ba, mu kaisu kotu sannan a sako su, wannan abu yana tayar min da hankali, kuma wannan abu na bata min rai ba kadan ba."

Da yake magana game da matakin da ya dauka na ganin an dakile matsalar, Dikko ya shaida cewa, ya tuntubi ma'aikatar shari'a ta jihar Kano domin bayyana kokensa.

A cewarsa:

"Na ziyarci mai shari'a na jihar Kano, kuma na yi magana dashi, to sai ya nuna min cewa za su yi wani abu akai, sannan kuma maganar sababbin dokokin nan na jihar Kano, su ma suna daya daga cikin abubuwan da suka kawo cikas a irin wannan abubuwan.

Kara karanta wannan

Tashin hankali: 'Yan fashi da makami sun dura wani coci, sun yiwa fasto da mabiyansa tas

"Mun yi magana dashi kuma kwamishina na shari'a, shima ya yi alkawarin yin wani abu a kai, to amma har yanzu dai ga shi har karshen zama na a Kano ya zo, amma har yanzu ba a samu mafita a kai ba."

'Yan sanda ba sa sakin 'yan ta'adda haka siddan, inji CP Dikko

Da aka tambaye kan zargin da ake yawan yiwa 'yan sanda na sakin 'yan ta'adda bayan kama su, Dikko ya yi karin haske, ya ce sam ba laifin 'yan sanda bane a zahirance.

A kalamansa:

"Tunda na zo garin nan, duk wani mai laifi da muka kama, zan tabbatar an kai shi kotu. Kuma mai kula da sashin bincike imma zai ba da belin wani sai ya tuntube ni. Kuma idan ya tuntube na duba sai na ce masa wannan a kai shi kotu, a ba da belinsa a kotu. Wallahi kuma hakan ne, sai an kai shi kotun sai kuma a ba da belinsa.

Kara karanta wannan

Bidiyo: Mu muka tallata Buhari, dole mu fito mu fadi gaskiya, Naburaska ya cashe gwamnati

"Wannan laif ne na hukumar shari'a, wanda muna kira ga hukumar shari'a da su yi duk abin da za su taimakawa jami'ain tsaro, abin na da karya gwiwa."

Kuje: Yadda ‘Yan ta’adda suka raba kudi, suka yi wa’azi kafin sakin ‘Yan gidan yari

A wani labarin, ‘yan ta’addan da suka kai hari a gidan gyaran hali da ke Kuje a garin Abuja, sun rabawa wadanda ke tsare kudi kafin su sake su domin su sulale.

Daily Trust ta fitar da rahoto a ranar Juma’a 8 ga watan Yuli 2022 da ya bayyana cewa ‘yan ta’addan sun ba mutane kudi da nufin samun na hawa mota.

Fiye da mutane 800 suka tsere a daren Laraba daga gidan mazan, amma ana cewa an kamo 400 a cikinsu, wasunsu kuma su na ta dawowa a kan gashin kansu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel