Yadda Matar Aure Ta Kashe Mijinta Ta Hanyar Daba Masa Wuka A Jihar Adamawa

Yadda Matar Aure Ta Kashe Mijinta Ta Hanyar Daba Masa Wuka A Jihar Adamawa

  • Matar aure mai shekaru 20 ta kashe mijinta a jihar Adamawa bayan wani sabani ya gibta a tsakaninsu
  • Yan sanda a jihar Adamawa sun kama Caroline Barka wacce ta dabawa mijinta wuka saboda ya yi dare a waje sannan ya dawo cikin maye
  • Rikici ya kaure tsakanin wacce ake zargi da marigayi mijinta bayan ya fada kan dansu mai shekara daya da ke kwance yana barci

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Adamawa - Rundunar yan sandan jihar Adamawa a ranar Juma’a, 22 ga watan Yuli, sun kama wata uwargida mai shekaru 20 kan zargin dabawa mijinta mai shekaru 38 wuka har lahira.

Kamar yadda DSP Suleiman Nguroje, kakakin yan sandan jihar ya bayyana, rigima ya shiga tsakanin wacce ake zargin mai suna Caroline Barka, mazauniyar Angwan Tamiya, karamar hukumar Madagali, da mijinta, Barka Dauda.

Kara karanta wannan

Shan Giya Da Yawon Dare: Matar Aure Yar Shekara 20 Ta Kashe Mijinta A Adamawa

Fada ya kaure a tsakaninsu ne bayan marigayin ya dawo gida cikin maye sannan ya fada kan dansu mai shekara daya wanda ke kwance kan gado, Daily Trust ta rahoto.

Yan sanda
Matar aure ta kashe mijinta ta hanyar daba masa wuka a jihar Adamawa Hoto: Premium Times
Asali: UGC

Wani bangare na sanarwar ya ce:

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

“Ta fusata da kasancewarsa cikin maye, dabi’ar yin dare a waje da kuma rashin daukar dawainiyarta a matsayinsa na miji, sai fada ya kaure tsakanin wacce ake zargin da marigayin wanda ya kai ga har ta caki mijin nata. Sakamakon haka ya fadi cikin wani hali sannan aka kwashe shi zuwa asibiti inda aka tabbatar da mutuwarsa.”

Nguroje ya kara da cewar yan sanda a karamar hukumar Madagali sun kama wacce ake zargin bayan samun rahoto daga wani dan uwan mamacin, rahoton LIB.

Ya bayyana cewa kwamishinan yan sandan jihar, CP S K Akande, ya umurci mataimakin kwamishinan yan sanda (Sashin bincike) da ya dauki shari’ar sannan ya tabbatar da an hukunta wacce ake zargin daidai da laifinta.

Kara karanta wannan

Kannywood: Bidiyon Jaruma Umma Shehu Da Diyarta Suna Tikar rawa Ya Haddasa Cece-kuce

Bidiyon magidanci da kanwar matarsa a bandaki, yayi alkawarin siya mata iPhone idan ta kwanta da shi

A wani labarin, wani bidiyo mai bada mamaki ya bayyana kuma ya janyo maganganu bayan an ga mijin yaya yana rokon kanwar matarsa da ta kwanta da shi.

Boyayyar kamara ce ta nadi bidiyon wacce wani ya dasa ta yayin da mutumin ya ja budurwar zuwa bandaki.

A bidiyon, an ga magidancin ya zube kasa guiwa bibbiyu yana rokon budurwar amma fafur tace bata san wannan zancen.

Asali: Legit.ng

Online view pixel