Bidiyon magidanci da kanwar matarsa a bandaki, yayi alkawarin siya mata iPhone idan ta kwanta da shi

Bidiyon magidanci da kanwar matarsa a bandaki, yayi alkawarin siya mata iPhone idan ta kwanta da shi

  • A wani bidiyo da boyayyar kamara ta nada, an ga wani magidanci yana rokon kanwar matarsa kan cewa yana son kwanciya da ita
  • Sai dai yarinyar ta jajirce inda tace ba zata taba cin amanar yayarta ba wacce ke matukar kyautata mata ta hanyar kwanciya da shi
  • Tuni magidancin yace zai siya mata iPhone in har ta bashi kanta, amma budurwar da ya ritsa a bandaki tace ba za ta iya ba kwata-kwata

Wani bidiyo mai bada mamaki ya bayyana kuma ya janyo maganganu bayan an ga mijin yaya yana rokon kanwar matarsa da ta kwanta da shi.

Boyayyar kamara ce ta nadi bidiyon wacce wani ya dasa ta yayin da mutumin ya ja budurwar zuwa bandaki.

Magidanci da kanwar matarsa
Bidiyon magidanci da kanwar matarsa a bandaki, yayi alkawarin siya mata iPhone idan ta kwanta da shi. Hoto daga @gistreel
Asali: Twitter

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kara karanta wannan

Bidiyon Yadda Wata Amarya Da Mahaifinta Suka Fashe Da Kuka A Wajen Liyafar Bikinta

A bidiyon, an ga magidancin ya zube kasa guiwa bibbiyu yana rokon budurwar amma fafur tace bata san wannan zancen.

Amma sai dai, ta kusa bada kai bori ya hau bayan yayi mata alkawarin siya mata waya kirar iPhone wacce ta dade tana mafarkin mallaka.

A martanin wasu 'yan Najeriya bayan sun ga bidiyon, sun musanta cewa duk shirya wa aka yi, amma wasu sun yadda na gaskiya ne tare da caccakar magidancin ta yadda baya iya danne maitarsa.

Kalla bidiyon:

Budurwa ta kai karar magidanci wurin matarsa bayan yayi mata karyar mutuwar matarsa

A wani labari na daban, Dani Bose, kyakyawar Baturiya ta fallasa wani mutum da suka kwashe shekaru 30 da matarsa da aure amma yake neman matan banza a waje.

Budurwa mai shekaru 21 kuma tauraruwa TikTok ta bayyana yadda magidancin yayi ikirarin cewa matarsa ta mutu kuma yake son su hadu domin lalata.

Kara karanta wannan

Tana Tara Kudi: Bidiyon Yadda Wata Mata Ta Koma Rayuwa Cikin Motarta Saboda Ba Za Ta Iya Biyan Kudin Haya Ba

A bidiyon, ta bayyana yadda matarsa ta neme ta kuma tace tana son ta gwada mata cewa ko mijinta da suka yi shekaru 30 suna tare yana cin amanarta.

Asali: Legit.ng

Online view pixel