Bidiyon Jaruma Umma Shehu Da Diyarta Suna Tikar rawa Ya Haddasa Cece-kuce

Bidiyon Jaruma Umma Shehu Da Diyarta Suna Tikar rawa Ya Haddasa Cece-kuce

  • Akwai kusanci da shakuwa mai karfi a tsakanin Jaruma Umma Shehu ta Kannywood da diyarta Amira
  • Umma Shehu ta wallafa wani sabon bidiyo a shafinta na soshiyal midiya inda suke tikar rawa da rera waka tare da babbar 'yarta budurwa
  • Mabiya shafinta sun tofa albarkacin bakunansu, ta birge wasu yayin da wannan tarbiya sam bata yiwa wasu ba

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Jama’a sun tofa albarkacin bakunansu bayan bayyana wani bidiyo na shahararriyar jarumar masana’antar shirya fina-finan Hausa ta Kannywood, Umma Shehu.

A cikin bidiyon wanda jarumar da kanta ta daura a shafinta na Instagram mai suna official_ummahshehu, an gano Umma tare da diyarta mai suna Amira suna rawa tare da rera wata wakar Turanci.

Umma Shehu
Bidiyon Jaruma Umma Shehu Da Diyarta Suna Tikar rawa Ya Haddasa Cece-kuce Hoto: Premium Times
Asali: UGC

Yayin da wannan shakuwa da kusanci nasu ya birge da dama, wasu na ganin sam wannan bata dace da tarbiyar uwa ta gari ba.

Kara karanta wannan

Biki Ake Na Manya: Bidiyoyi Daga Shagalin Bikin Fatima Shettima Da Angonta Sadiq Bunu

Wannan ba shine karo na farko da jama’a ke caccakar jarumar ba a kan irin wadannan halayya nata na son sharholiya da kuma sako yarta a ciki.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Hakazalika tana daya daga cikin jarumai mata da ake bibiyar duk wani motsinsu domin ganin sun yi dan kuskure.

Kalli bidiyon a kasa:

Martanin mabiya shafin nata

aminusbono ya yi martani:

“Kunyi matukar birgeni idan naga daughter ta da mamanta haka nake ganin su kamar kawaye suyi ta bani dariya cikin farin ciki ina adduar Allah yayi musu Albarka yasanya su cikin Aminci duniya da lahira”

bachob40_227 ya ce:

"Barewa batayi gudu"

alameensanni ya ce:

"Amma dai anji kunya"

harunakolina ya yi martani:

"Yau ga uwar banza a nan"

abdulrashiddanladiabubakar ya ce:

"Girma yayi gaddama"

been_sheikh ya tofa:

"Wannan tarbiya tayi"

outlow_killer_makashi ya ce:

"Ikon ALLAH tweens kenan"

Kara karanta wannan

Buhari ga 'yan Najeriya: Ku zabi Tinubu don ci gaba da shan jar miyar da nake baku

souleymane0_ ya yi martani:

"Kamar ‘ya kamar uwa"

Mutane su gama aibatani a zo ranar lahira su ga na shige Aljanna na barsu - Umma Shehu

A wani labarin, mun kawo a baya cewa Umma Shehu, ta yi tsokaci a kan aibata ta da wasu mutane ke yi, sakamakon kallo da suke yi mata a matsayin mai aikata sabon Ubangiji.

A wani bidiyo da sashin Hausa na BBC ya fitar, an jiyo jarumar tana fadin cewa ita da zunubinta ta damu ba da na wani ba sannan kuma cewa duk a laifukan da take aikatawa bata hada Allah da wani.

Jarumar ta kuma bayyana cewa tana cika salollinta guda biyar, don haka Allah mai gafara ne, idan ta roke sa cikin kuka zai yafe mata.

Asali: Legit.ng

Online view pixel