Yan Bindiga Sun Yi Barazanar Sace Buhari Da El-Rufai A Sabon Bidiyo

Yan Bindiga Sun Yi Barazanar Sace Buhari Da El-Rufai A Sabon Bidiyo

  • Tsagerun yan bindigar da suka sace fasinjoji a jirgin kasan Abuja-Kaduna sun saki sabon bidiyo tare da azabtar da mutanen da ke hannunsu
  • Yan bindigar sun yi barazanar kama Shugaban kasa Muhammadu Buhari da gwamnan jihar Kaduna, Mallam Nasir El-Rufai
  • Yan ta'addan sun kumasha alwashin sace manya-manyan jami’an gwamnati da ‘yan siyasa, ciki har da sanatoci

Yan makonni bayuan farmakin da aka kaiwa ayarin motocin shugaba Muhammadu Buhari a jihar Katsina, yan ta’adda sun yi barazanar yin garkuwa da shugaban kasar na Najeriya.

An dai farmaki tawagar tsaron shugaban kasar a hanyarsu ta zuwa mahaifar Buhari da ke Daura gabannin bikin Sallah.

Mutane biyu sun jikkata a harin wanda aka ce fadar shugaban kasar ta dakile.

Yan bindiga
Yan Bindiga Sun Yi Barazanar Sace Buhari Da El-Rufai A Sabon Bidiyo Hoto: channelstv.com
Asali: UGC

Kamar yadda jaridar Daily Trust ta rahoto, a cikin sabon bidiyon da suka saki, yan bindigar wadanda suka sace fiye da fasinjoji 60 a jirgin kasar Kaduna a ranar 28 ga watan Maris, sun yi barazanar sacewa da kuma halaka Buhari da gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai.

Kara karanta wannan

Yan Bindiga Sanye Da Kayan Sojoji Sun Kashe Fitaccen Jigon Jam'iyyar PDP Har Lahira

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Yan ta’addan sun kuma bugi kirjin cewa sai sun lalata kasar, su kashe sauran fasinjojin jirgin kasa da ke hannunsu sannan su siyar da sauran.

A bidiyon da jaridar Leadership ta wallafa a Youtube, an jiyo daya daga cikin yan ta’addan na cewa:

“Kasar nan sai mun ruguzata gaba daya, da mutanen cikinta gaba daya. Idan za ku zo ku yi addini ku zo ku yi amma muna nan muna kafa kanmu, addinin nan sai ya yadu a ko’ina.
"Ka sani sai mun kama ka da hannunmu mun kawo ka jejin nan mun yanka ka, El-Rufai Kadunan gaba daya babu shi. Ku sani gani cikin dajin nan, kuma ku dube ni da kyau ba wai baku sanni ba, kun sanni kun turawa dubiya gaba daya wai duk inda aka ganni a kama ni, toh nima duk inda na ganku, nima a nemo min ku nima ina so in kama ku gaba dayanku, zan kashe ku.”

Kara karanta wannan

Kannywood: Bidiyon Jaruma Umma Shehu Da Diyarta Suna Tikar rawa Ya Haddasa Cece-kuce

Ya ci gaba da cewa:

“Kamar yadda aka siyar da yan matan Chibok, haka za mu siyar da wadannan a matsayin bayi. Idan kun ki yarda da bukatarmu, za mu kashe wadannan sannan mu siyar da sauran. Da izinin Allah, El-Rufai, Buhari, sai mun kawo ku nan.”

Yan Bindiga Sanye Da Kayan Sojoji Sun Kashe Fitaccen Jigon Jam'iyyar PDP a Bayelsa

A wani labarin, Ogbolosingha, mai shekaru 53, ma'aikaci ne a gwamnatin jihar Bayelsa a sakateriya da ke Okordia/Zarama Development Board, The Nation ta rahoto.

Rahotanni sun nuna cewa an kashe shi ne awanni bayan sallamo matarsa daga asibiti.

Lamarin, da ya faru a Mechanic Village kan hanyar Edepie-Imiringi road a Yenagoa, babban birnin jihar ta janyo hatsaniya a unguwar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel