"Bisa Tsautsayi Na Zama Shugaban Najeriya", Tsohon Shugaban Kasa Obasanjo

"Bisa Tsautsayi Na Zama Shugaban Najeriya", Tsohon Shugaban Kasa Obasanjo

  • Tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya bada labari mai ban sha'awa game da rayuwarsa
  • A cewar tsohon shugaban na mulkin soja, duk abin da ya cimma a rayuwa baiwa ce daga Allah
  • Amma, dattijon na kasa ya ce abu daya da har yanzu ya ke alfahari da shi shine kasancewarsa manomi

Tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya ce duk abubuwan da ya aikata da ya kuma samu bisa tsautsayi ne amma banda noma, rahoton PM News.

Tsohon shugaban na mulkin soja, wanda aka zaba a karkashin mulkin farar hula a 1999, ya bayyana hakan ne a ranar Asabar, 23 ga watan Yuli, a wani shirin rediyo na kai tsaye tare da Segun Odegbami a Eagles 7 Sports 103.7 FM, Abeokuta.

Olusegun Obasanjo
"Bisa Tsautsayi Na Zama Shugaban Najeriya", Tsohon Shugaban Kasa Obasanjo. Hoto: PM News.
Asali: Facebook

Obasanjo ya ce yana son noma

Kara karanta wannan

Atiku Abubakar: Ban Taba Zama Fiye Da Wata Daya a Dubai Ba

Obasanjo ya bayyana cewa tuntuni yana alfahari da kasancewarsa manomi, rahoton The Punch ya kara da cewa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Odegbami ya tambayi Obasanjo ya yi magana a kan abin da ya kira "soyayyarsa da noma."

A martaninsa, tsohon shugaban kasar ya ce:

"Bana son kalmar da ka yi amfani da ita 'soyayya da noma'. Ni manomi ne. Me ka ke nufi da soyayya? Duk abin da na yi a rayuwa ta tsautsayi ne. Abin da kawai ba tsautsayi ba shine noma. Kuma ka kira hakan soyayya? A'a! Me ka ke nufi da soyayya?
"Ka san yadda na fara. A kauye aka haife ni kuma na girma. Tsautsayi ta sa na tafi makaranta. Mahaifi na ya ce, ba za ka yi wani abu daban ba? Don haka, na fara noma.
"Idan ka duba kasashen da suka cigaba, sun cigaba ne da noma. Na farko, saboda samun tsaro na abinci; na biyu, sarrafa abin da suke nomawa a gonakinsu, wanda shine farkon kafa masana'antu. Na uku, mu fitar da shi zuwa kasashen waje don samun kudin shiga; na hudu a matsayin hanyar samar da ayyuka ga matasa."

Kara karanta wannan

Atiku: Tikitin Musulmi Da Musulmi Yasa Ban Amince Da Tinubu Ba Lokacin Da Yake Son Zama Abokin Takara Na

Hotunan Obasanjo Ya Kwaso Fasinjoji A Adaidaita Sahu Ya Kayyatar Da Al'umma

A wani rahoton, tsohon shugaban kasar Najeriya Olusegun Obasanjo a murnar cikarsa shekaru 85 ya tuka babur din adaidaita sahu a titunan Abeokuta.

Tsohon shugaban kasar ya cika shekaru 85, a ranar 5 ga watan Maris, an hange shi yana daukan fasinjoji a cewar wasu hotuna da aka gani a shafin Daniel Sync Olusanya, wani mai daukan hotu dan Najeriya mazaunin Landan daga Ijebu, Jihar Ogun.

Asali: Legit.ng

Online view pixel