Atiku: Tikitin Musulmi Da Musulmi Yasa Ban Amince Da Tinubu Ba Lokacin Da Yake Son Zama Abokin Takara Na

Atiku: Tikitin Musulmi Da Musulmi Yasa Ban Amince Da Tinubu Ba Lokacin Da Yake Son Zama Abokin Takara Na

  • Atiku Abubakar, dan takarar shugaban kasa na PDP a zaben 2023 ya ce gujewa tikitin musulmi da musulmi yasa ya ki yarda Bola Tinubu ya yi masa mataimaki a zaben 2007.
  • Tsohon mataimakin shugaban kasar na Najeriya ya ce Najeriya kasa ce mai addinai da al'adu daban-daban don haka ya kamata a rika daidaito wurin zaben shugabannin kasar.
  • Atiku ya ce har yau Tinubu abokinsa ne amma abokantarsu ba za ta hana su samu mabanbanta ra'ayoyi ba a bangaren siyasa da wasu harkokin

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar ya ce kauracewa tikitin musulmi da musulmi yasa ya ki yarda Asiwaju Bola Tinubu ya yi masa mataimaki a zaben shekarar 2007, The Cable ta rahoto.

Atiku, wanda ya yi wa tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo mataki daga 1999 zuwa 2007, ne ya bayyana haka yayin wata hira da aka yi da shi a ARISE TV a ranar Juma'a.

Kara karanta wannan

2023: Ku kwantar da hankali, za fa ku ci zaben nan, Buhari ga Tinubu da Shettima

Abubakar Atiku
Atiku: Tikitin Musulmi Da Musulmi Yasa Ban Amince Da Tinubu Ba Lokacin Da Yake Son Zama Abokin Takara Na. Hoto: @thecableng.
Asali: Twitter

Atiku ya samu matsala da Obasanjo a yunkurinsa gadon kujerarsa, amma daga baya ya samu tikitin takarar shugaban kasa a karkashin jam'iyyar Action Congress, AC, jam'iyyar da Tinubu ya taimaka wurin kafa ta bayan 'guguwar' siyasa ta tarwatsa gwamnonin AD da aka zaba a 1999.

Kusan karshen wa'adinsa na biyu a matsayin gwamnan Legas, Tinubu ya fara aikin kafa jam'iyyar AC, wacce Babatunde Fashola, Ministan Ayyuka da Gidaje ya ci zaben a karkashinta ya gaji Tinubu.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Yayin rikicinsa da Obasanjo, Atiku ya fita daga PDP ya koma AC inda ya samu tikitin takarar shugaban kasa.

Amma, ya zo na uku a zaben da marigayi Shugaban Kasa Umaru Yar'adua ya lashe kuma Muhammadu Buhari na ANPP ya zo na biyu.

A hirar da aka yi da shi a ARISE, Atiku ya ce tikitin musulmi da musulmi wanda yanzu ake takkadama a kai ce ta sa bai zaɓi Tinubu matsayin mataimakinsa ba.

Kara karanta wannan

Dan takarar APC Tinubu: Dole ne na kwaci Najeriya a 2023 don na samar da ayyukan yi

"Ban taɓa yarda da tikitin musulmi da musulmi ba. Najeriya kasa ce mai kabilai da addinai daban-daban don haka ya kamata akwai daidaito na addini a shugabancin mu," in ji shi.

Tinubu, wanda zai fafata da Atiku a zaben shekarar 2023, ya zaɓi Kashim Shettima, musulmi a matsayin abokin takararsa kuma hakan ya janyo takkadama.

Da aka tambayi alakarsa da Tinubu, Atiku ya ce, "Har yanzu aboki na ne amma abota bata nufin ba za mu iya samun banbanci na siyasa ba."

Atiku Abubakar: Ban Taba Zama Fiye Da Wata Daya a Dubai Ba

A wani rahoton, Atiku Abubakar, dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ya ce bai taba zama fiye da wata guda ba a Dubai ba bayan lokacin da ya karatun digirinsa na biyu.

Tsohon mataimakin shugaban kasar na Najeriya ya bayyana hakan ne a yayin hira da aka yi da shi a Arise TV a ranar Juma'a.

Asali: Legit.ng

Online view pixel