Hotunan Obasanjo Ya Kwaso Fasinjoji A Adaidaita Sahu Ya Kayyatar Da Al'umma

Hotunan Obasanjo Ya Kwaso Fasinjoji A Adaidaita Sahu Ya Kayyatar Da Al'umma

  • Don murnar cikarsa shekaru 85, tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya tuka adaidaita sahu a titunan Abeokuta
  • Baba Iyabo, kamar yadda aka saba kiransa ya raba wa matasa baburan adaidaita a Ogun don murnar zagayowar ranar haihuwarsa
  • A cewar hotunan da suka bazu a shafukan sada zumunta, an hangi Obasanjo yana daukan fasinjoji a yayin da ya ke tafiya a hankali tare da jami'an tsaro

Ogun, Abeokuta - Tsohon shugaban kasar Najeriya Olusegun Obasanjo a murnar cikarsa shekaru 85 ya tuka babur din adaidaita sahu a titunan Abeokuta.

Tsohon shugaban kasar ya cika shekaru 85, a ranar 5 ga watan Maris, an hange shi yana daukan fasinjoji a cewar wasu hotuna da aka gani a shafin Daniel Sync Olusanya, wani mai daukan hotu dan Najeriya mazaunin Landan daga Ijebu, Jihar Ogun.

Kara karanta wannan

Hotunan Dawowar Buhari Gida Abuja Bayan Kai Ziyara Portugal

Tsohon shugaban kasa Obasanjo.
Hotunan Obasanjo Ya Zama Direban Adaidaita A Abeokuta Sun Kayyatar. Hoto: Daniel Sync Olusanya.
Asali: Facebook

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

A cewar wani rahoto da The Cable ta wallafa, Obasanjo, a watan Yuni, ya raba wa mutum 85 baburan adaidaita sahu a yayin murnar cikarsa shekaru 85.

Legit.ng ta tattaro cewa akwai jami'an tsaro biye da tsohon shugaban kasar Obasanjo a lokacin da ya ke dauke da fasinjojin.

Magoya baya da dama sun rika bin tsohon shugaban kasar suna masa jinjina a yayin da ya ke tuka adaidaita sahun.

Olusanya a shafinsa na Facebook ya ce:

"Don murnar Baba@85 da kuma tallafawa matasa (karkashin jagorancin Cibiyar Karatu ta Olusegun Obasanjo) tsohon shugaban kasa Cif Olusegun Obasanjo ya tuka daya daga cikin "Keke Napep" din (a.k.a Maruwa/Tricycle) zuwa Kuto Abeokuta tare da fasinjoji.
"An fara tafiyar ne daga gidan Obasanjo da ke OOPL zuwa karkashin gada ta Kuto suka dauki fasinjoji (wanda suka rika murna cewa tsohon shugaban kasa ya tuka su) abin sha'awa ne.

Kara karanta wannan

Wike Ya Saki Hoto Da Magana Mai Boyayyen Ma'ana Bayan Jita-Jitar Ganawarsa Da Tinubu a Faransa

"Baki daya, matasa 85 sun amfana da kyautan adaidaita sahu daga shirin Baba@85."

Mun Baka Awa 48: PDP Za Ta Yi Wa Obasanjo Fallasa Idan Bai Yi Karin Haske Kan Maganan Da Ya Yi Kan Atiku Ba

A wani labarin, Jam'iyyar Peoples Democratic Party, PDP, ta bukaci tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya yi karin haske kan kalaman da ya furta kan dan takarar shugaban kasarta, Atiku Abubakar ne cewa ya yi kuskure wurin zabensa (Atiku) a matsayin mataimakinsa a 1999, Nigerian Tribune ta rahoto.

A cewar PDPn, idan tsohon shugaban kasar bai yi karin haske kan kalaman da aka danganta da shi ba cikin awa 48, jam'iyyar za ta fada wa yan Najeriya ainihin ko wanene Obasanjo.

Asali: Legit.ng

Online view pixel