Hotuna da bidiyo: Jiragen saman hamshaƙai 11 sun dira a Maiduguri don bikin ɗan marigayi Umaru Musa Ƴaradua

Hotuna da bidiyo: Jiragen saman hamshaƙai 11 sun dira a Maiduguri don bikin ɗan marigayi Umaru Musa Ƴaradua

  • A kalla jiragen sama 11 na hamshakan masu kudi, 'yan siyasa da kasaitattun mutane daga sassan kasar nan har da ketare ne suka dira a Maiduguri a yau Asabar
  • Ana sa ran zuwa wasu duk don halartar shagalin bikin auren Shehu 'Yaradua, 'dan marigayi shugaba Umaru Musa Yar'adua da Yacine Sheriff
  • Bikin ya dauka kala sakamakon yadda aka tsara bikin 'yan gatan kuma 'ya'yan manyan gidaje masu fadi a ji a kasar nan

Maiduguri, Borno - A kalla jiragen sama mallakin hamshakan masu kudin Najeriya da 'yan siyasa 11 ne suka hallara a garin Maiduguri, jihar Borno domin daurin auren Shehu, 'dan marigayi shugaban kasan Najeriya, Alhaji Umaru Musa Yar'adua.

A yau 23 ga watan Yulin 2022 ne Shehu ya aura kyakyawar rabin ransa, diyar Honarabul Mohammed Nur Sheriff mai suna Yacine.

Kara karanta wannan

Atiku Tantirin Maƙaryaci Ne, In Ji Tinubu, Ya Tona Abin Da Ya Faru Kan Tikitin Musulmi Da Musulmi a 2007

Yacine da Shehu
Hotuna da bidiyo: Jiragen saman hamshaƙai 11 sun dira a Maiduguri don bikin ɗan marigayi Umaru Musa Ƴaradua. Hoto daga lindaikejisblog.com
Asali: UGC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Bikin Aure
Hotuna da bidiyo: Jiragen saman hamshaƙai 11 sun dira a Maiduguri don bikin ɗan marigayi Umaru Musa Ƴaradua. Hoto daga lindaikejisblog.com
Asali: UGC

Shehu mai shekaru 29 ya samu digirinsa na fako a fannin tattalin arziki daga makarantar kasuwanci ta Schellhammer dake Spain kuma yayi digirinsa na biyu a fannin mu'amalar kasashe daga jami'a Webster dake Netherlands.

Zukekiyar amaryarsa Yacine mai shekaru 22 tana da digiri na farko daga jami'ar Surrey daka Ingila inda ta karanci Hospitality Management.

Bikin Aure
Hotuna da bidiyo: Jiragen saman hamshaƙai 11 sun dira a Maiduguri don bikin ɗan marigayi Umaru Musa Ƴaradua. Hoto daga lindaikejisblog.com
Asali: UGC

Hotuna: Ango ya zabi doki matsayin babban abokinsa a aurensa, har amarci ya tafi da shi

A wani labari na daban, wani masoyin doki ya yanke hukuncin amfani da ingarman dokin da yafi kauna a matsayin babban abokinsa a ranar aurensa kuma har ya kai ga tafiya da shi cin amarci.

Paul Boyles mai shekaru 47 ya shirya yadda dokinsa ya taya shi karbar aure a ranar aurensa sa masoyiyarsa Kay mai shekaru 48.

Kara karanta wannan

Bakin Ciki Biyu A Yayin Da Yan Bindiga Suka Kashe Jigon PDP a Jihar Arewa, Suka Bindige Dansa

A matsayin dokin na babban abokin, an sanya dokin mai suna Erik dan kunne tare da sirdi na musamman.

Asali: Legit.ng

Online view pixel