Hotuna: Ango ya zabi doki matsayin babban abokinsa a aurensa, har amarci ya tafi da shi

Hotuna: Ango ya zabi doki matsayin babban abokinsa a aurensa, har amarci ya tafi da shi

  • Wani ango dan asalin Ingila mai suna Paul, ya zabi ingarman dokinsa ya zama babban abokinsa ranar aurensa
  • Bayan nan, sabon angon mai shekaru 47 tare da amaryarsa Kay mai shekaru 48 sun tafi da dokin cin amarci na kwana 11 a Wales
  • Paul yace ana sauran wata 6 aurensu ne ya samu matukar shakuwa da dokin Erik, wanda hakan yasa ba zai iya rabuwa da shi ba

Wani masoyin doki ya yanke hukuncin amfani da ingarman dokin da yafi kauna a matsayin babban abokinsa a ranar aurensa kuma har ya kai ga tafiya da shi cin amarci.

Paul Boyles mai shekaru 47 ya shirya yadda dokinsa ya taya shi karbar aure a ranar aurensa sa masoyiyarsa Kay mai shekaru 48.

A matsayin dokin na babban abokin, an sanya dokin mai suna Erik dan kunne tare da sirdi na musamman.

Kara karanta wannan

Daukar Dala Babu Gammo: Yadda Dan Najeriya Ya Ajiye Aikin Da Ake Biyansa Miliyan N24, Ya Koma Turai Yin Digirgir

Ango mai doki
Hotuna: Ango ya zabi doki matsayin babban abokinsa a aurensa, har amarci ya tafi da shi. Hoto daga dailymail.co.uk
Asali: UGC

Erik ya raka sabbin ma'auratan zuwa shagalin cin amarcinsu na tsawon kwanaki 11 bayan auren.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Paul da Kay sun fito ne daga yankin Durham dake Ingila kuma sun siye shi a shekarar da ta gabata tare da adana shi a turkensa inda ake kula da shi.

Sun ce bayan Paul ya shaku da dokin, basu da wani zabi da ya wuce su tabbatar da shi matsayin babban abokin ango a ranar bikinsu.

Paul wanda manajan kanti ne a Lidi, yace: "Da farko ba zan sanya kowa a matsayin babban aboki ba.
"A aure, abu mafi wuya shine zama babban abokin ango, dole ne ka kasance mai barkwancin. Ba za ka matsawa kowa kamar hakan ba.
"Ana sauran watanni shida bikin ne na samu wata irin shakuwa da Erik kuma nayi tunanin cewa ina son ya halarci bikin."

Kara karanta wannan

Atiku Abubakar: Ban Taba Zama Fiye Da Wata Daya a Dubai Ba

Ya boye zabinsa na babban abokin ango daga amaryarsa har sai ranar bikin.

Ya kara da cewa: "Na so siya masa fulawoyi, babban sirri ne. Shi ke dauke da zobban. Da farko Kay ta tsorata bayan da ta ga Erik."
Ma'auratan sun yi watsi da shirinsu na zuwa Italy cin amarci inda a maimakon hakan suka tafi Wales da babban aboki Erik, inda Paul ya kara da cewa: "Ba a kowacce rana bane kake daukan babban abokinka zuwa cin amarci."
Kay ta kara da cewa: "A wurinmu, labari ne mai cike da farin ciki. Rana ce ta musamman a gare mu."

Asali: Legit.ng

Online view pixel