Yan Bindiga Sun Bi Dan Majalisar PDP Gidansa Sun Bindige Shi Har Lahira a Adamawa

Yan Bindiga Sun Bi Dan Majalisar PDP Gidansa Sun Bindige Shi Har Lahira a Adamawa

  • Wani labari da zai jefa yan Najeriya cikin bakin ciki shine harin ya yan bindiga suka kai a Jihar Adamawa
  • Yan bindiga a ranar Asabar sun halaka mataimakin shugaba na karamar hukumar Song, Jihar Adamawa, Hon Ishaya Bakano
  • A bangare guda, rundunar yan sandan jihar ta Adamawa ta tabbatar da afkuwar harin

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Jihar Adamawa - Wasu gungun yan bindiga, a safiyar ranar Asabar sun kashe mataimakin shugaba na karamar hukumar Song, Jihar Adamawa, Hon. Ishaya Bakano.

Taswirar Jihar Adamawa.
Yan Bindiga Sun Bi Dan Majalisa Gidansa Sun Bindige Shi Har Lahira a Adamawa. Hoto: @MobilePunch.
Asali: UGC

Ana zargin mutuwar Hon Ishaya, wanda ke wakiltar gundumar Gudu Mboi, kisar gilla ne, domin yan bindigan da suka kutsa gidansa da ke Bannga sun tafi jim kadan bayan sun bindige shi har lahira.

Mai magana da yawun rundunar yan sandan Jihar Adamawa, Suleiman Yahaya Nguroje ya tabbatarwa Punch Metro afkuwar lamarin.

Kara karanta wannan

Hotunan fitattun 'yan siyasar Najeriya da hamshakan da suka halarci auren diyar Kashim Shettima

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Kakakin yan sandan ya ce lamarin ya faru da asubahin yau, kuma jami'an tsaro suna iya kokarinsu domin ganin sun kama wadanda ake zargin.

Tashin Hankali: 'Yan Ta'adda Sun Sace Mutune 50 A Jihar Neja

Yan ta'adda sun sace mutane hamsin daga garin Kuchi, a karamar hukumar Munya na Jihar Neja, The Punch ta rahoto.

A cewar shugaban kungiyar matasan Shiroro a Jihar Neja, Sani Kokki, wanda ya bayyana hakan cikin sanarwar da ta bawa The Punch, ya ce an sace mutanen ne misalin karfe 2 na dare yayin da ake ruwan sama.

Dan Bindigan Da Aka Nada Sarauta a Zamfara, Aleru, Ya Kashe Mutane 100 A Katsina, In Ji Rundunar Yan Sanda

A gefe guda, rundunar Yan Sandan Jihar Katsina ta tabbatar da cewa shugaban yan bindiga, Ado Aleru, wanda aka nada sarauta ranar Alhamis da ta gabata a masarautar Yandoto Daji a Zamfara, har yanzu suna nemansa ruwa a jallo.

Kara karanta wannan

Shirin 2023: Buhari ya shiga wata ganawa mai muhimmanci da Shettima da su Tinubu

Rundunar yan sandan ta ce ana zargin Alero da kashe mutane 100 mazauna Jihar Katsina, kamar yadda Leadership ta rahoto.

Kakakin rundunar, Gambo Isah, ne ya bayyana hakan yayin da ya ke martani kan nadin sarautar da aka yi wa shugaban yan bindigan a Zamfara.

Isah ya ce rundunar ta ayyana neman Aleru ruwa a jallo don laifuka da suka hada da kisa, ta'addanci, fashi da makami da garkuwa da mutane a Jihar Katsina.

Asali: Legit.ng

Online view pixel