Yadda Dan Najeriya Ya Ajiye Aikin Da Ake Biyansa Miliyan N24, Ya Koma Turai Yin Digirgir

Yadda Dan Najeriya Ya Ajiye Aikin Da Ake Biyansa Miliyan N24, Ya Koma Turai Yin Digirgir

  • Wani dan Najeriya ya yi watsi da aikin da ake biyan sa naira miliyan 24 duk shekara, ya tattara kayansa ya kowa turai yin digiri na biyu
  • Matar mutumin wacce take manajar banki itama ta ajiye aikinta sannan ta bi mijinta tare da yara
  • Wasu yan Najeriya a shafin Twitter sun kasa gaskata labarin, amma wasu sun ce ya yi hakan don yaransa ne

Jama'a sun yi cece-kuce a shafin Twitter bayan samun labarin wani dan Najeriya da ya bar aikin da ake biyansa makudan kudade a Najeriya sannan ya koma Turai da zama.

Kamar yadda ya zo a labarin wanda Oluwakayode Bakre ya wallafa, mutumin na samun naira miliyan 24 a matsayin albashi duk shekara a nan gida Najeriya, amma sai ya yanke shawarar yin kaura zuwa Turai.

Kara karanta wannan

Atiku Abubakar: Ban Taba Zama Fiye Da Wata Daya a Dubai Ba

Wallafar Twitter da jirgi
Yadda dan Najeriya ya ajiye aikin da ake biyansa miliyan N24, ya koma Turai yin digirgir Hoto: @kayodebakre8 and Aaron Foster/Getty Images
Asali: UGC

Ya koma Turai tare da iyalinsa

Hakazalika, an ce matarsa manajar banki ce kuma suna rayuwar jin dadi a cikin wani katafaren gida na alfarma a Lekki.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

An tattaro cewa shi da matar tasa za su yin digiri na biyu a Birtaniya, inda suka koma da zama. Wasu yan Najeriya sun kasa gaskata labarin.

Oluwakayode ya rubuta a Twitter:

“Albashin 24m duk shekara. Katafaren gida na alfarma a Lekki. Yara biyu. Mata na aiki a matsayin manajar bankin zamani. Amma sun ajiye aiki da fara digiri na biyu a UK. Ban fahimci wasu daga cikin wadannan abubuwan ba.”

Jama’a sun yi martani

@akingbadegroup ya ce:

“24M ya maganar bayan biyan kudin haraji, 20m, naira na rage daraja fa kimanin 25% duk shekara kafin Disamba albashinka zai sauka zuwa ace 18m. Kana biyan kudin makaranta na ban mamaki kan yara biyu a Lekki duk shekara 3m. Ka kona man diesel da sauran abubuwa. Da albashin N2m duk wata da kyar kake iya ajiye 250k."

Kara karanta wannan

'Dan Tinubu, Obi Cubana, da wasu matasa 3 mafi Kudi cikin matasan Najeriya

@chidi_adaugo ya yi martani:

"Su suka sani! idan na samun wannan, ina shakku idan zan so sauya waje? zan biya kudin samu ingantaccen lafiya dan kariya maimakon naje yin bauta a kasar wani. Sai dai idan akwai aiki da ke jina a chan."

@istee01 ya ce:

“Gaskiya wannan shawara ta yin kaura ya zarce fahimtata. Da ina tunanin kaura ta masu safarar mutane ne. Amma yadda mutum zai bar rayuwar jin dadi sannan ya koma yin aikin masaki a Turai ya fi karfina."

Bidiyo: Ƴan achaɓa sun ritsa abokin aikinsu da yayi shekara 3 bai yi wanka ba, sun masa wanka a titi

A wani labarin kuma, wani 'dan achaban kasa Ghana wanda ya yadu a kafafen sada zumunta kan tsabar kazantarsa ya ba mutane mamaki.

A bidiyon da ke ta yawo, an ga abokan aikinsa sun yi masa wankan dole a binar jama'a, @alreadyviralofficial suka wallafa bidiyon inda aka ga matashin yana kokarin kubcewa daga wurin wankan

Kara karanta wannan

Yanzu Yanzu: Tinubu ya magantu a kan manyan Bishop-Bishop da aka gani a wajen gabatar da Shettima

Wani mutum da ke rike da waya inda yake nadar yadda ake yi wa 'dan achaban wanka ya yi bayanin dalilin da yasa matasan suka dauka wannan matakin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel