Bidiyo: Ƴan achaɓa sun ritsa abokin aikinsu da yayi shekara 3 bai yi wanka ba, sun masa wanka a titi

Bidiyo: Ƴan achaɓa sun ritsa abokin aikinsu da yayi shekara 3 bai yi wanka ba, sun masa wanka a titi

  • Wani matashin 'dan achaban kasar Ghana wanda ya kwashe tsawon shekaru 3 bai yi wanka ba, yayi wankan dole a bainar jama'a
  • An shirya biki na musamman domin yi masa wanka ba tare da saninsa ba a wani bidiyo da ya yadu mai bada dariya
  • Duk da yayi duk yadda zai yi domin tserewa daga hannun abokan aikinsa da suka shirya yi masa wankan, sai da suka samu nasara

Wani 'dan achaban kasa Ghana wanda ya yadu a kafafen sada zumunta kan tsabar kazantarsa ya ba mutane mamaki.

A bidiyon da ke ta yawo, an ga abokan aikinsa sun yi masa wankan dole a binar jama'a, @alreadyviralofficial suka wallafa bidiyon inda aka ga matashin yana kokarin kubcewa daga wurin wankan.

Okada Men
Duƙununu: Ƴan achaɓa sun ritsa abokin aikinsu da yayi shekara 3 bai yi wanka ba, sun masa wanka a titi. Hoto daga @alreadyviralofficial
Asali: Instagram

Dalilin da yasa 'yan achaban suka yi masa wankan dole

Kara karanta wannan

Bidiyon tsohon limamin Harami tsuke cikin kananan kaya a kan tsadajjen babur ya janyo cece-kuce

Wani mutum da ke rike da waya inda yake nadar yadda ake yi wa 'dan achaban wanka ya yi bayanin dalilin da yasa matasan suka dauka wannan matakin.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

A kalamansa yake cewa: "Baya kaunar wanka, ya yi sama da shekaru uku yanzu haka rabon shi da yin wanka. Wanne irin mutum ne wannan? Warin da yake yi kawai ya isa yasa a gane amma a yau ko yana so, ko baya so. sai yayi fes."

Bidiyon tsohon limamin Harami tsuke cikin kananan kaya a kan tsadajjen babur ya janyo cece-kuce

A wani labari na daban, bidiyon limamin babban masallacin Annabi, Sheikh Adel al-Kalbani yana kan babur din Harley Davidson sanye da kananan kaya ya janyo hankalin jama'a masu tarin yawa.

A bidiyon da aka nada a Snapchat, an ga al-Kalbani zaune a kan babur din a gefen titi inda yake sanye da riga dake dauke da tutar Amurka. Yana murmushi tare da farin ciki yayin da ake nadar bidiyon.

Kara karanta wannan

Ganin Ta da Nayi Babu kaya Ya sa Nayi Mata Fyade Inji Matshi Da aka Kama Da Mahaukaciya

Tuni sunan tsohon limamin ya dinga yawo a Twitter inda yayi tashe tun bayan sakin bidiyon a soshiyal midiya a ranar Litinin, lamarin da ya janyo cece-kuce.

Asali: Legit.ng

Online view pixel